Gwamnonin Najeriya sun ce Babban Bankin Najeriya ba wata basira ba ce da ya ƙirƙiro sauya launin kuɗi, sai kawai ƙwace ne ƙiriƙiri bankin ya yi wa kuɗaɗen jama’a, ya tara ya kimshe a hannun sa.
Gwamnonin Najeriya sun ce CBN ya gaggauta janye wa’adin da zai daina amsar tsoffin kuɗi, a ƙyale kowa ya ji da abin da ya ishe shi.
Sun bayyana haka a taron ganawa da su ka yi a Abuja ranar Asabar.
‘Ƙwacen kuɗi Emefiele ya yi wa jama’a ba canjin kuɗi ba’ -Gwamnonin Najeriya:
Cikin sanarwar da aka fitar bayan taron, gwamnonin sun ce “CBN abin da CBN ke ci gaba da yi, ba canjin kuɗi ba ne, ƙwacen kuɗaɗe ne kawai da rana tsaka su ke yi wa jama’a. Amma wannan tsiya da ba ta yi daidai dokar musayar kuɗaɗe ta Sashe na 20(3) na Doka wadda CBN ya ginu a kai, ta shekarar 2007.
“Ƙwacen kuɗaɗe ne mana domin an ƙwace kuɗaɗen jama’a, su kuma waɗanda ke sabbi babu su kwata-kwata babu alamar su. Waɗanda aka ce an buga ba su wadata ba.
Wannan kakkausan bayani na ƙunshe ne a cikin takardar bayan taron da Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto ya sa wa hannu.
Gwamnonin sun cimma wannan matsayar ce ganin irin halin ƙuncin da aka jefa ‘yan Najeriya ba rashin kuɗi, musamman ma
talakawa.
Gwamnonin na Najeriya sun gargaɗi CBN cewa wannan bahangurɓar canjin kuɗi za ta haifar da karayar tattalin arzikin Najeriya.
Sun ce fito da wannan tsarin taƙaita hada-hada da takardun kuɗaɗe ba abu ne da zai yi tasiri yanzu-yanzu a ƙasar nan kamar ɗibar wuta ba.
Sun ce idan ba a yi da gaske an shawo kan lamarin ba, to CBN zai kawo mummunan ruɗani ga tattalin arzikin Najeriya, wanda idan ya karye, to ɗora shi sai fa maɗoran asali.