Hedikwatar Tsaro ta bayyana cewa Sojojin Najeriya sun samu nasarar damƙe ɗaya daga cikin gogarman shirya fashin jirgin ƙasa kan hanyar Abuja-Kaduna Kaduna, wanda aka yi a ranar 27 Ga Maris, 2022.
Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Musa Ɗanmadami ne ya bayar da sanarwar a lokacin da ya ke yin taron manema labarai a ranar Alhamis, a Abuja.
A taron wanda a kan yi duk bayan makonni biyu ana sanar wa manema labarai irin nasarorin da Sojojin Najeriya su ka samu a wuraren da su ke bayar da kariyar tsaro da yaƙi da ta’addanci da ‘yan bindiga.
Ɗanmadami ya ce wanda ake zargi ɗin na ɗaya daga cikin ‘yan ta’adda uku da sojoji su ka kama a ƙauyen Damba, cikin Ƙaramar Hukumar Chikun, ranar 14 Ga Fabrairu, 2023.
Ya ce a samamen da sojoji su ka kai masu, sun kama babura biyu, wayar hannu biyu, Dalar Amurka 5,000, wasu kuɗaɗen daban da kuma tarkacen kayayyaki daban-daban.
Haka kuma Ɗanmadami ya ce sojojin da ke sintiri sun bindige ‘yan bindiga bakwai a Ungwan Birni cikin Ƙaramar Hukumar Kajuru duk a Jihar Kaduna.
Ya ce an samu tulin albarusai 153 da jigida bakwai da sauran nau’ukan muggan makamai a hannun ‘yan ta’addar da aka bindige ɗin.
Bayan harin jirgin ƙasan da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum takwas, tare da yin garkuwa da 168, an riƙa sakin su kashi-kashi bayan an biya maƙudan kuɗaɗen fansa.
Rukunin ƙarshe da su ka rage a hannun su dai sun samu kuɓuta ne a ranar 5 Ga Oktoba, 2022.