Hedikwatar rundunar tsaron ƙasa DHQ ta bayyana cewa sojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 77 a Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya a cikin makonni biyu da suka wuce.
Darektan yaɗa labarai na rundunar tsaron Najeriya manjo-janar Musa Danmadami ya sanar da haka a Abuja ranar Alhamis.
Danmadami ya ce rundunar Operation Hadin Kai’ dake aiki a yankin Arewa maso Gabas sun kashe Boko Haram da ‘yan kungiyar ISWAP 56, sun kama wasu 26 sannan sun ceto mutum 59 da aka yi garkuwa da su.
Ya Kuma ce sojojin sama sun kashe Ƴan ta’adda da dama wani ruwan bama-baman da suka yi wa maɓoyar mahara dake Gogore, Damboa, Tumbun Dila, Arege da wasu wurare dake Yammacin Tumbuns a jihar Borno.
Danmadami ya ce mahara tare da iyalen su 340 sun mika wuya da a cikin su akwai maza 12, mata 133 da yara 195.
Sannan a ranar 27 ga Janairu sojojin sun kai wa mahara a kauyen Yuwe dake karamar hukumar Konduga a jihar Borno hari inda suka kashe ‘yan ta’ada 17
Sojojin sun kwace bindiga kiran GPMG guda daya, bam grenade l 36 da harsasai 77.
Sannan a ranar 30 ga Janairu sojojin sun kashe mahara uku sun ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su a farmaki da suka kai a kauyukan dake kananan hukumomin Bama da Mafa.
A ranar 4 ga Fabrairu sojoji sun Kai wa maboyar ‘yan ta’adda hari a kauyen Balange dake kusa da dajin Sambisa inda suka kashe mahara 5 sannan suka ceto mutum 55 da ke tsare a hannun su.
A Arewa maso Yamma Danmadami ya ce Operation Hadarin Daji sun kashe mahara 16 sannan sun kama wasu mutum 7 a yankin.
“Dakarun sun kama bindigogi kira AK-47 12, bindigogin hannu 16, bindiga kirar FN daya da harsasai masu yawa.
A Arewa ta Tsakiya Danmadami ya ce Operation Safe Haven da Operation Whirl Stroke’ sun kashe ƴan ta’adda biyar, sun kama wasu guda 10 sannan da mutum daya mai siyar wa mahara da bindigogi.