Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya roƙi al’ummar Jihar Ribas cewa su jefa ƙuri’ar su daidai yadda gwamnatin jihar ta tsara waɗanda ta ke so a zaɓa.
Wike ya roƙe su kada su zaɓi shugaban da idan ya hau mulki zai kwance masa zani a kasuwa, a a kashe karkashin siyasar Wike ɗin.
Ya ce su ɗan saurara shugabannin siyasar jihar na yankuna da mazaɓu daban-daban za su sanar wa kowa waɗanda za a zaɓa.
Wike ya yi wannan kira a ranar Asabar, a wurin kamfen ɗin PDP reshen jihar Ribas, a Fatakwal.
“Tun daga ƙananan hukimomi har zuwa mazaɓu, za a riƙa bin ku ana sanar da ku wanda ya kamata ku zaɓa.
“Saboda haka idan ku na so na tsira da mutuncin siyasa ta, har a daɗe ana damawa da ni, to ku bi umarnin zaɓen wanda mu ke so ku zaɓa.
“Mu dai ba za mu zaɓi waɗanda idan sun hau mulki za su kashe ni ba. Ba za mu zaɓi waɗanda su ka ce idan sun ci mulki za su ɗaure ni ba. Shin za ku bari su kashe ni ne?
“Ko za ku zaɓi waɗanda ba su ƙaunar su ka mu na numfashi a duniya?” Inji Wike.
Waɗannan jawabai na Wike su na cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Wike mai suna Kelvin Ebiri ya sa wa hannu kuma ya aiko wa PREMIUM TIMES.
Wike dai ya ce ba zai zaɓi ɗan takarar PDP Atiku Abubakar. Yayin da shi kuma Gwamna Samuel Ortom na Benuwai ya ke wa Peter Obi kamfen.
A ranar Asabar ɗin dai Wike ya jinjina wa Gwamnonin APC saboda jajircewar da su ka yi cewa 2023 a zaɓi ɗan kudu ya yi shugabancin Najeriya. Ya ce hakan shi ne adalci da kyakkyawan zamantakewar al’umma domin a fahimci juna.
Discussion about this post