Lauyoyi da masu shigar da ƙara da Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja sun sun nuna ɓacin rai dangane da yadda ƙarancin sabbin kuɗaɗe na haifar masu cikas ta hanyar kasa tattara kundin bayanan shari’u a kotuna.
Wasu lauyoyin da aka yi hira da su a ranar Lahadi, sun nuna matuƙar damuwa yadda ƙarancin kuɗaɗe ke kawo masu tangarɗa wajen gudanar da aikin lauya.
Wani mai suna Cleansman Ogidi, wanda ke a Babbar Kotun Tarayya a Maitama, ya ce karancin kuɗi na haifar masu da jinkirin tattara bayanan zaman kotu ƙwarai da gaske.
Ya ce ya yi niyyar shigar da wata ƙarar neman kotu ta dakatar da wani abu, amma rashin kuɗin shigar da ƙara ya sa tilas ya haƙura.
Ya ce tun da matsalar ƙarancin sabbin kuɗi ta zo, su na fuskantar rashin kuɗin shigar da kararraki.
Ya ce kuma yanzu abin ba Babbar Kotu kaɗai ya shafa ba. Ya ce har da sauran kotuna a Abuja.
“Ba mu da kuɗaɗe a ƙasa na shigar da ƙara. Idan mu kace ta waya ko ta shiga intanet za mu riƙa tura kuɗaɗe su na ƙin tafiya, ko kuma matsalar ‘netwok’ ta sa ka yi ta turawa amma su ƙi shiga can. Waɗanda ka tura ɗin kuma an cire maka kenan, ba za’a dawo maka da su ba.
Yayin da ake tunanin samun sauƙin cewa a ci gaba da kai tsoffin kuɗi bankuna, sai CBN ya musanta sanarwar da aka ce ya ce bankuna su ci gaba da karɓar tsoffin N500 da N1000.
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya musanta iƙirarin da aka danganta da shi, inda aka ce ya ce a ci gaba da karɓar tsoffin kuɗaɗe na naira 500 da naira 1000.
CIkin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran CBN, Osita Newnisobi ya fitar a ranar Juma’a, CBN ya ce maganar ta bogi ce, kuma ƙarya aka yi wa bankin.
A ranar Juma’a ɗin ce dai wasu rahotanni su ka ruwaito CBN ya ce bankunan kasuwanci su ci gaba da karɓar naira 500 da naira 1000 tsoffi.
Haka ma har rahoton ya ce CBN ya ce aƙalla amma sai daga naira 500,000 za a karɓa a hannun mutum, kuma sau ɗaya tilo.
Sai dai kuma a martanin da bankin ya bayar a ranar Juma’a, CBN ya ce rahoton ƙarya ce kawai, ba ta umarci bankunan kasuwanci su ci gaba da karɓar tsoffin kuɗaɗen ba.
“Mu dai mu na nan a matsayin mu kan jawabin da Shugaban Ƙasa ya yi a ranar 16 Ga Fabrairu, 2023, don haka naira 200 kawai aka bai wa CBN umarnin ci gaba da amfani da ita a ƙasar nan har zuwa kwanaki 60 nan gaba, wato 10 ga Afrilu, 2023.
“Mu na kira ga jama’a su yi watsi da batun ci gaba da kai tsoffin naira 500 da naira 1000 banki, kai da ma duk wata sanarwa kan tsoffi da sabbin kuɗi in dai ba daga CBN aka yi sanarwar kai-tsaye ba.”
Daga nan CBN ya umarci kafafen yaɗa labarai su riƙa tabbatarwa su na tantance labarai kafin su buga.
Bincike ya tabbatar cewa ‘yan Najeriya masu ɗimbin yawa na ajiye da tsoffin kuɗaɗe saboda matsalar ƙarancin sabbin kuɗaɗe.
Tuni dai Kotun Ƙoli ta hana CBN ƙin tsoffin kuɗaɗe, amma kuma bankin ya yi kunnen-uwar-shegu da umarnin kotu.
Kasuwanci da harkokin yau da kullum manya da ƙanana duk nema su ke su tsaya cak, yayin da wasu da dama su ka taƙaita yin zirga-zirga maras dalili.
A ranar Alhamis Shugaba Buhari ya bada umarnin a ci gaba da karɓar tsoffin naira 200. Ranar Juma’a kuma aka riƙa watsa sanarwa a soshiyal midiya cewa bankunan kasuwanci su ci gaba da karɓar naira 500 da naira 1000. Amma daga baya sai CBN ya fito ya ƙaryata.