Sanata Ahmad Lawan ya koma kan kujerar sa ta Sanatan Yobe ta Arewa, bayan ya lashe ƙuri’u 91,318.
Ɗan takarar PDP Bello Ilu ne ya zo na biyu da ƙuri’u 22,849.
Wannan ne zaɓen na bakwai da Lawan ya lashe tun daga 1999 bai yi fashin zuwa majalisa ba.
Tsohon Ministan Neja Delta, Godswill Akpabio ya lashe kujerar Sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.
Ya samu ƙuri’u 115,401, shi kuma abokin adawar sa babban, Emmanuel Enoudem na PDP ya samu 69,838.
A Jihar Gombe kuwa tsohon Gwamna Ibrahim Danƙwambo na PDP ya kayar da Sanatan Gombe ta Arewa da kan kujerar, Sa’idu Alƙali na APC.
Ɗanƙwambo ya samu ƙuri’u 143,155, shi kuma Alƙali ya samu 77,948.
PREMIUM TIMES Hausa ta Bayar da labarin cewa guguwa ta tarwatsa garken wasu gwamnonin da su ka shiga takarar sanata.
Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Enugu ya sha ƙasa a takarar Sanatan Enugu ta Arewa da ya fito a ƙarƙashin PDP.
Ɗan takarar LP Okechukwu Ezea ne ya kayar da shi.
Ƙoƙarin Ugwuanyi na tafiya Majalisar Dattawa bayan kammala wa’adin mulkin shekara takwas bai yi nasara ba.
Ɗan takarar LP ya samu ƙuri’u 104,492, shi kuma Gwamna Ugwuanyi ya tashi da 46,948, bai ma kai rabin wanda ya kayar da shi ba kenan.
Shi kuwa ɗan takarar APC Ejike Eze ƙuri’u 6,816 kaɗai ya samu.
Irin yadda aka yi wa Ugwuanyi na Enugu, haka shi ma Ben Ayade ma Cross River ya sha kaye a hannun Sanatan da ke kan kujera a yanzu, Jarigbe Agom-Jarigbe.
Ayade Gwamnan APC ya sha kaye a hannun Jarigbe ɗan PDP, wanda ya lashe ƙuri’u 76,145, shi kuwa Ayade aka bar shi da 56,595.