Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na NNPP, Rabi’u Kwankwaso ya samu ƙuri’u 1,179,889 a jihar Kano.
Waɗannan yawan ƙuri’un sun tabbatar da cewa shi kaɗai ne ɗan takara ɗaya tilo wanda ya samu ƙuri’u miliyan ɗaya a jiha ɗaya, a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Wannan tarihi da Kwankwaso ya kafa ya nuna cewa babbar asara ce ga PDP, wadda rikicin cikin gidan da ya faru a cikin ta ne ya fusata Kwankwaso ficewa har ya koma NNPP ya fito takara.
Bola Tinubu na APC ya yi ƙoƙari sosai a Kano, inda ya samu ƙuri’u 773,528, sai kuma Atiku Abubakar na PDP ya kasa samun kashi 25% bisa 100% a jihar Kano, domin Kuwait Kuwait ƙuri’u 143,213 kaɗai a samu a faɗin jihar mai ƙananan hukumomi 44.
Discussion about this post