A safiyar Litinin aka bayyana sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 38 daga cikin 44 na jihar Kano.
Sakamakon da INEC ta fitar ya nuna ɗan asalin Jihar Kano mai takara ƙarƙashin NNPP, Rabi’u Kwankwaso ya samu 748,362, shi kuma Bola Tinubu na APC ya na da 464,133. Atiku Abubakar na PDP ya na na uku da ƙuri’u 86,162.
Peter Obi ya na da 8,926 kacal.
Can a Jihar Adamawa kuwa, Atiku ya lashe ƙananan hukimomi 11, Peter Obi 1, ana jiran sakamakon sauran 10.
Bayan kammala tattara sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 12 na Jihar Adamawa daga cikin 20 ɗin da jihar ke da su, Atiku Abubakar na PDP kuma ɗan asalin jihar ya lashe ƙananan hukumomi 11.
Peter Obi na LP ya lashe sakamakon Ƙaramar Hukumar Numan.
PDP ta lashe Lamurde, Gerei, Shelleng, Guyuk, Toungo, Ganye, Mayo-Belwa, Song, Demsa, Fufore da Yola ta Kudu.
Atiku ya samu ƙuri’u 213,117, APC kuma 99,898, sai LP 56,857. NNPP ta tashi da 3,609.
Sakamakon Jihar Gombe ya tabbatar da Atiku ya lashe dukkan ƙananan hukumomin Gombe, ya nunka Tinubu samun ƙuri’un jihar.
Ɗan takarar shugabancin ƙasa a PDP, Atiku Abubakar ya lashe dukkan ƙananan hukumomin Jihar Gombe 11.
Baturiyar Zaɓe Farfesa Maimuma Waziri ta bayyana Atiku ya samu ƙuri’u 319,123, shi kuma Bola Tinubu na APC ya samu 146,977.
A Ƙaramar Hukumar Gombe ce Atiku ya fi samun yawan ƙuri’u har 62,347, sai Akko 55,202, sai kuma Yamaltu Deba 38,479.
Discussion about this post