Hasalallun matasa sun ɓarke da zanga-zangar banka wa bankuna wuta a wasu biranen ƙasar nan, sakamakon ƙarancin sabbin kuɗaɗen naira 200, 500 da kuma 1,000.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Delta, Bright Edafe, ya ce matasa sun cinna wa bankuna biyu wuta a ƙananan hukumomin Udu cikin jihar Delta.
Ya ƙara da cewa baya ga bankunan biyu, an kuma ƙona motoci biyu.
“Mun samu nasarar kama mutum tara.” Ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa amma wajen ƙarfe 6:14 ƙura ta lafa, komai ya dawo daidai.
A Benin, babban birnin Jihar Edo, masu zanga-zangar sun kai wa bankuna hari, ciki har da bankunan Ecobank, First Bank da UBA. Haka dai Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Edo, Chidi Nwabuzor ya tabbatar.
Sun shiga har cikin farfajiyar bankin, su ka lalata asusun ATM da dama da kuma farfasa gilasan tagogi.” Inji Kakakin ‘Yan Sanda.
Sauran garuruwan da matasa su ka yi wa bankuna zanga-zangasun haɗa da Uyo, babban birnin Akwa Ibom.
Gwamnan Jihar Delta kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Atiku Abubakar a PDP, Ifeanyi Okowa, ya roƙi jama’a a kai zuciya nesa.
Shi kuwa Gwamna Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo, cewa ya yi canjin kuɗi ya rage wa APC daraja da ƙima a idon masu zaɓe mai zuwa.
Gwamna Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo ya ce ƙaƙudubar canjin kuɗi ta shafa wa APC kashin kaji, martaba da kwarjinin jam’iyyar ya fara zubewa, a lokacin da zaɓen 2023 ke gabatowa.
Akeredolu ya yi wannan bayani a lokacin da ya ke karɓar shugabannin matasan APC, waɗanda su ka kai masa ziyara ƙarƙashin jagorancin Seyi Tinubu, ɗan Bola Tinubu mai wa APC takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa.
Gwamna Akeredolu ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya gaggauta soke tsarin sauya launin kuɗin da ya ƙirƙiro.
Akeredolu ya ce kamata ya yi a bar sabbin kuɗi da tsoffin a riƙa amfani da su a lokaci ɗaya.
Daga nan ya nuna damuwa da mamakin ganin yadda duk da Kotun Ƙoli ta ce a ci gaba da amfani da tsoffin kuɗin a makon da ya gabata, sai ga shi CBN da sauran jama’a sun ce lokacin amfanin su ya wuce.
Ya ce ba a ƙirƙiro canjin kuɗi lokacin da ya dace ba. Musamman matsalar canji ta riski matsalar wahalar fetur da tsadar sa, sai su ka haɗu su ka ƙara wa APC baƙin jini.
“Matsala ta afka wa jam’iyyar mu a yanzu. APC sai baƙin jini ta ke ƙara yi, saboda matsalar canjin kuɗi da matsalar fetur.
“Kada mu yaudari kan mu. Shin tilas sai a wannan lokacin ne za a canja kuɗin? Wannan tsari bai kamata a wannan lokaci ba kwata-kwata. A soke tsarin kawai, a bar tsoffin kuɗaɗe su ma a ci gaba da amfani da su.
“Masu babura, ‘yan taksi da bankuna sun daina karɓar tsoffin kuɗaɗe. Kotun Ƙoli ta ce a ci gaba da karɓar tsoffin kuɗaɗe, amma kowa ya ƙi bin umarnin kotu.
“Tun lokacin da Gwamnan CBN ya fito takarar shugaban ƙasa mu ka ce a cire shi, amma aka yi biris da mu.
“Emefiele bai cancanci zama kan shugabancin CBN ba. Mutumin da ya nemi yin takarar shugaban ƙasa, ai kowa ya san ƙafar-ungulu zai yi mana a yanzu.”
Akeredolu ya jinjina wa Seyi Tinubu, kuma ya ƙara jaddada goyon bayan su a Bola Tinubu.
Discussion about this post