Gwamnatin Najeriya ta nemi Kotun Ƙoli ta yi fatali da ƙarar da gwamnoni uku su ka shigar, waɗanda ke so a hana CBN daina karɓar tsoffin kuɗaɗe a ranar 10 Ga Fabrairu.
Gwamantin Tarayya ta shigar da wannan sabuwar ƙarar ce sa’o’i kaɗan bayan Kotun Koli ta bada umarnin a ci gaba da karɓar tsoffin kuɗi har zuwa ranar da za ta yanke hukunci tukunna.
Gwamnatin Buhari ta ce Kotun Ƙoli ba ta da hurumin ikon sauraren ƙarar da gwamnonin uku su ka shigar a gaban ta.
Gwamnati ta ce babu ruwan Kotun Ƙoli da wannan karankatakaliya, domin ba rikici ba ne tsakanin gwamnatocin jihohi da gwamnatin tarayya, rikici ne tsakanin hukumar gwamnati ita ɗaya tilo, wato CBN.
A kan haka gwamnati ta ce Kotun Ƙoli ba ta da hurumin sauraren ƙarar.
Gwamnonin uku su ne na jihohin Kaduna, Kogi da Zamfara.
Gwamnatin Tarayya ta ce kamata ya yi a fara shari’ar tun daga Babbar Kotun Tarayya tukunna.
Kotu ta aza ranar 15 Ga Fabrairu ta zama ranar yanke hukunci.
A dalilin wannan hukunci da ak yanke, mutanen Najeriya sun yi ta tofa albarkacin bakin su game da wannan umarni na Kotu sun ce abinda gwamnonin suka yi jihadi ne ga talakawa domin an shiga cikin tsanani matuka a sassana kasar nan.
Discussion about this post