Tsohon Kwamishinan Tarayya na Yaɗa Labarai, dattijo Edwin Clark, ya nemi Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta ya gaggauta sauka daga takarar mataimakin shugaban ƙasa na Atiku Abubakar a PDP, a zaɓen 25 ga Fabrairu, 2023 da ke tafe.
Clark ya yi wannan kiran ne a taron manema labarai ranar Alhamis, a Abuja.
Ya ce takarar mataimakin shugaban ƙasa da Okowa ke yi a PDP ta keta martabar yarjejeniyar Gwamnonin Kudu da su ka cimma cewa tilas sai dai mulki ya bar Arewa ya koma Kudu a 2023.
“Okowa ya yi wa sauran gwamnonin Kudu butulci da kuma kudu ɗin baki ɗayan ta.
“Okowa ya ci amanar mu tunda har ya yarda ya zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa ga Atiku Abubakar. Ba don na ɗaure masa gindi ba, babu yadda za a yi ya ci zaɓen gwamnan Jihar Delta.
“Abin da ya ba mu mamaki shi ne yadda Okowa ya maƙale wa Atiku Abubakar ya na yi masa takarar mataimakin shugaban ƙasa, ba tare da ya tuntuɓe mu ba.
“Ai mutumin nan ya yaudare mu. Mun zauna mun amince cewa Okowa mayaudari ne, don haka ba za mu sake amincewa da shi ba.”
Clark, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Masu Kishin Neja-Delta (PANDEF), ya aika wa Okowa wasiƙa a ranar 2 Ga Fabrairu, inda ya shaida masa cewa Atiku ba zai yi nasara a zaɓen 2023 ba.
Clark ya zargi Okowa da kamfatar kuɗaɗen Jihar Delta ya na ciyar da Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta Atiku Abubakar. Daga nan ya nemi Okowa ya roƙi afuwar ɗaukacin al’ummar Kudu, domin ya ci amanar su.
“A yau ina tabbatar da cewa babu wani gwamna da aka taɓa yi a Jihar Delta wanda ya kai ka yin mulkin kama-karya, tun bayan kafuwar jihar cikin 1991.
“To ka sani ko ka yi addu’a, Ubangiji ba zai karɓa ba, saboda ka ci amanar ɗaukacin al’ummar kudancin Najeriya.” Inji Clark.