Rundunar Yaƙin APC ta bayyana cewa zargin da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi cewa akwai maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa, tuggu ne kawai ya ke yi don ya tattago sojoji su yi juyin mulki a Najeriya.
Kakakin Rundunar APC, Dele Alake ya bayyana cewa babu ruwan Obasanjo da harkar zaɓe.
A ranar Litinin ce Obasanjo ya tayar da tsohon tsimi, ya yi zargin akwai harƙalla a zaɓen shugaban ƙasa, amma a kai zuciya nesa.
Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi zargin cewa an cukurkuɗa sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.
Obasanjo ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya sa sake bibiyar gaba ɗayan yadda aka tattara sakamakon zaɓen.
Haka Obasanjo ya bayyana a cikin wata wasiƙar da shi da kan sa ya sa wa hannu a ranar Litinin.
Ya yi zargin cewa “yawancin sakamakon zaben da aka tattara ba tare da na’urar tantance masu katin shaidar rajistar zaɓe (BVAS da Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe (Server) ba, ba su nuna haƙiƙanin gaskiyar abin da ‘yan Najeriya su ka zaɓa ba.”
Obasanjo dai na ɗaya daga cikin masu goyon bayan jam’iyyar LP, wadda Peter Obi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.
PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa jam’iyyar LP da PDP da wasu ‘yan adawa sun fice daga Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe ta INEC a Abuja, a ranar Litinin.
Sun fice ne bayan sun zargi INEC da ƙin sakin sakamakon zaɓe a manhajar iREV.
Jam’iyyun sun ce ƙin fitar da sakamakon a iREV kamar yadda Dokar INEC ta tilasta a yi, ya nuna cewa akwai alamun zai yiwu a damalmala lissafin ƙuri’un.
A cikin sanarwar Obasanjo, ya jinjina wa Buhari a kan matsayin da ya ɗauka na tabbatar da cewa ya bar wa Najeriya gadon sahihin zaɓe.
Sai dai kuma ya yi kira ga Buhari ya ceto ƙasar nan daga hatsarin da ta ka iya faɗawa sakamakon zaɓe.
Discussion about this post