Gwamnatocin jihohin Kaduna da Kogi da Zamfara sun kai ƙarar gwamnatin tarayya Kotun Ƙolin suna masu rokon kotun da ta dakatar da gwamnatin tarayyar karkashin shugaba Muhammadu Buhari da gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele daga aiwatar da tsarin wa’adin amfani da tsoffin takardun kuɗi da kuma sabbin kuɗi da gwamnatin ta kirkiro da shi
Gwamnatocin nnsun ce sunnyi haka ne dubi da yadda mutanen kasa suka faɗa cikin tsananin mawuyacin hali sakamokon matsalar ƙarancin sabbin kuɗin suka ce ya jefa al’umomin jihohin su.
BBC HAUSA ta ruwaito cewa, Buƙatar da lauyan jihohin uku, AbdulHakeem Uthman Mustapha (SAN) ya gabatar wa kotun, ta nuna cewa jihohin arewacin ƙasar uku na bukatar Kotun ƙolin da ta tsayar da gwamnatin tarayya tare da hana CBN da bankunan ƙasar aiwatar da tsarin daina amfani da tsoffin takardun kuɗi zuwa wa’adin 10 ga watan Fabrairu da CBN ɗin ya saka.
Wadanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da kwamishinonin shari’a na jihohin uku, inda shi kuma ministan shari’a na ƙasar Abubakar Malami ne zai wakilci gwamnatin tarayya a shari’ar.
Masu shigar da ƙarar su ce tun bayan bayyana fara amfani da sabbin takardun kuɗin, ake samun matsalar ƙaracin sabbin kuɗin a jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara, kuma mutanen da suka kai tsoffin takardun kuɗin nasu bankuna, na shan matuƙar wahala kafin samun kuɗaɗen daga bankunan, a wasu lokutan ma ba sa samun kuɗin domin gudanar da rayuwarsu ta yau-da-kullum.
Sun ƙara da cewa wa’adin kwana 10 da gwamnatin tarayya ta ƙara ba zai isa ba wajen warware matsalar da ake fuskanta ta ƙarancin takardun kuɗin.
Discussion about this post