Rundunar Sibul Difens NSCDC reshen jihar Zamfara sun kama wasu matasa hudu da suka nemi yin garkuwa da ‘yar shekara biyu a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Ikor Oche ya sanar da haka a wata takarda da ya saka wa hannu a garin Gusau.
Oche ya ce jami’an tsaron sun kama wadannan matasa ne yayin da suke kokarin sace wata ‘yar shekara biyu a Angwan Shado dake cikin garin Gusau ranar 21 ga Janairu.
“Da aka gabatar da mutanen gaban manema labarai a hedikwatar hukumar Shugaban hukumar Muhammad Muazu ya ce an kama matasan yayin da suke kokarin sace Hauwa’u Masaud mai shekara biyu wace ke hannun yayanta Umalkaidi Shahibilu ‘yar shekara 13.
“Umalkaidi ta ce tana tafiya zuwa wurin da aka aike ta sai wani dake sanye da bakaken kaya da bincike ya gano sunan sa Muslim Sani ya zo ya fizgi Hauwa’u daga hannun ta ya tsare zuwa wani kangon ginin inda sauran abokan ke laɓe suna jiran sa.
Bayan an kama su an kuma gane wasu biyu daga cikin su.
Sai dai sun ce ba sace yarinyar suka yi ba sun bugu ne da tabar wiwi ba su ma san me suke yi ba a lokacin.
Sai dai kuma jami’an tsaron bata gamsu da abinda suka faɗi ba. Sun ce za a ci gaba da bincike.
Tuni an mika yarinyar ga iyayen ta.
Discussion about this post