Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sikiru Akande ya sanar da ya bayyana haka a taron manema labarai ranar a garin Yola.
Akande ya ce rundunar ta kai mutum 208 daga cikin yawan da ta kama din.
Ya ce rundunar ta kama wadannan mutane kan laifukan garkuwa da mutane, fashi da makami, satar shanu da dai sauran su.
Akande ya ce jami’an sun kama wadannan mutane da naurorin janareta, talabijin, bindigogi kirar hannu da bindigogi AK-47.
Akande ya gode wa mutanen jihar kan mara wa rundunar baya da suke yi don ganin ta kamo batagari irin haka.
Ya ce wadanda rundunar ta kama za ta tabbatar cewa an yanke musu hukunci bisa ga laifin da suka aikata sannan za ta ci gaba da kokari wajen ganin ta kamo sauran bata garin da suke damun mutane a jihar.
Discussion about this post