Ɗan takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin APC, Bola Tinubu, ya ƙaryata rahoton da wata jarida mai suna Peoples Gazette ta buga, inda ta ce shi ne ya ke gwara kan gwamnoni da na Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, har su ke ƙin bin umarnin sa.
Jaridar ta buga cewa Tinubu ne ya zuga wasu gwamnoni har su ka fito su na sukar Buhari, tare da bayar da umarnin a ci gaba da kashe tsoffin naira 500 da naira 1,000 a jihohin su.
Gwamna Nasir El-Rufai na daga cikin gwamnonin da suka kai Buhari ƙara kotu, kuma ya fito ya yi sanarwar a ci gaba da kashe tsoffin kuɗaɗe a jihar Kaduna, har sai an ga hukuncin da Kotun Ƙoli ta zartas tukunna a ranar 22 ga Fabrairu, 2023.
Shi ma Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano, ya fito ya ragargaji Buhari, har ya zarge shi da ƙoƙarin rushe APC, jam”iyyar da ta kai shi ga zama shugaban ƙasa har zango biyu.
Sai dai kuma Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta Bola Tinubu, ta ce jaridar Peoples Gazette ƙarya ta ke yi, babu ruwan Tinubu da abin da ke faruwa tsakanin Buhari da wasu gwamnoni.
Cikin sanarwar da Bayo Onanuga ya fitar, ya ce Tinubu bai taɓa bayar da wannan umarnin ba.
Jaridar ta yi iƙirarin cewa Mashawarcin Rundunar Yaƙin a Fannin Sadarwa, Dele Alake ne ya bayar da umarnin a madadin Tinubu.
Sai dai kuma Onanuga ya ce ƙarya jaridar ke wa Alake, bai furta haka ɗin ba.
Tuni dai ake ta watsa wannan zargi da ake wa Tinubu a shafukan sada zumunta musamman na WhatsApp.
Sanarwar ta ce tun lokacin da maganar canjin kuɗi ta fara tsami Tinubu ya rigaya ya bayyana hanyoyi shida waɗanda ya ce ya kamata a bi domin a samu maslaha. Daga nan kuma bai ƙara cewa komai ba, kuma bai ce wa wani ya ƙara cewa komai ba.
“Kuma ya sha yin taruka da Shugaban Ƙasa a kan wannan batun. Don haka gwamnonin da ke bijire wa Shugaban Ƙasa da kan su sun ce su na dogara ne da umarnin da Kotun Ƙoli ta bayar.”
Sanarwar ta nemi jaridar ta janye labarin da ta buga, kuma ta nemi afuwar Tinubu.
Sai dai kuma sanarwar ba ta ce komai ba dangane da maganganun dukan ƙirjin da irin su El-Rufai ke yi ba, inda su ke cewa idan Tinubu ya ci zaɓe zai soke tsarin canjin sabbin kuɗi da taƙaita cirar kuɗaɗe a bankuna da ATM, wanda gwamnatin Buhari ta ƙaƙaba.