Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna ya nuna matuƙar rashin jin daɗin yadda mutane su ka ƙi yin tururuwar fitowa jefa ƙuri’ar zaɓen shugaban ƙasa, musamman a cikin garin Kaduna.
Gwamnan ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai daidai lokacin da ya ke kan layin tantance masu katin shaidar rajistar zaɓe, a Rumfar Zaɓe ta 024, Mazaɓar Ward 7 da ke Unguwar Sarki, Kaduna.
Ya ce ya yi takaicin ganin yadda babu jama’a sosai a wasu rumfunan zaɓe.
“Damuwa ta shi ne mutane sun ƙi fitowa su yi zaɓe. Abu ne fa daga shekara huɗu sai kuma bayan shekara huɗu mutum zai sake samun wannan damar. Saboda haka ya kamata a riƙa ɗaukar wannan dama da muhimmanci.
“Shugabannin da ku ka zaɓa ne fa za su jagorance ku a ƙasa da jiha da ƙananan hukumomi har tsawon shekaru huɗu.
“Ku tuna duk lokacin da ka ƙi yin zaɓe, to ka bai wa jam’iyyar adawa ko jam’iyyar da ba ta ka ba ƙuri’u biyu ne a ɓagas, inji El-Rufai.
Gwamnan ya jinjina wa INEC musamman da ta yi tunanin ƙirƙiro fasahar amfani da na’urar tantance masu rajistar zaɓe (BVAS).