Jam’iyyar APC ta bayyana cewa abin takaici a ji dattijo kamar Olusegun Obasanjo, wanda ya yi shugabancin ƙasar nan, maimakon ya iya bakin sa, sai ya riƙa maganganu irin na ‘yan tasha, waɗanda za su iya kawo babbar barazana ga ɗorewar dimokraɗiyya a ƙasar nan.
APC ta ce Obasanjo ya riƙa kafto maganganun da ba su dace ba don kawai ya na so ya cimma wata ɓoyayyar manufar sa.
APC ta ce ta yi mamaki duk da zargin da Obasanjo ya yi ta nanatawa an yi, amma ya kasa kawo ko da wuri ɗaya inda zai tabbatar wa INEC cewa ta yi ba daidai ba.
Jam’iyyar APC ta ce duk abin da Obasanjo zai faɗa ai ba abin mamaki ba ne, domin tun a ranar 1 Ga Janairu, 2023 ya bayyana cewa shi ɗan takarar LP, Peter Obi ya ke goyon baya.
Daga nan jam’iyyar ta tunatar cewa Obasanjo har kira ya yi wa matasa su yi fitar-farin-ɗango domin su zaɓi LP da Peter Obi.
APC ta ce a jihar Ogun har a rumfar zaɓen Obasanjo ta kayar da Peter Obi. “Amma yadda Obasanjo ya fito ya na tayar da jijiyar wuya, to zaɓe ba zai zama sahihi a wurin sa ba, sai fa idan Peter Obi ne aka ce ya yi nasara baki ɗaya.
“Shin sakamkon zaɓen Legas ko na Delta ne waɗanda LP ta lashe?”
PREMIUM TIMES ta buga labarin da Obasanjo ya yi zargin cewa akwai harƙalla a zaɓen shugaban ƙasa, amma a kai zuciya nesa.
Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi zargin cewa an cukurkuɗa sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.
Obasanjo ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya sa sake bibiyar gaba ɗayan yadda aka tattara sakamakon zaɓen.
Haka Obasanjo ya bayyana a cikin wata wasiƙar da shi da kan sa ya sa wa hannu a ranar Litinin.
Ya yi zargin cewa “yawancin sakamakon zaben da aka tattara ba tare da na’urar tantance masu katin shaidar rajistar zaɓe (BVAS da Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe (Server) ba, ba su nuna haƙiƙanin gaskiyar abin da ‘yan Najeriya su ka zaɓa ba.”