Duk wani abin da ya biyo bayan sauya launin kuɗi da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya yi, ba abin mamaki ba ne, domin tun farko sai da masu hankali da hangen nesa su ka yi tsinkayen faruwar hakan.
Jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin halin ƙarancin sabbin kuɗaɗe bayan an raba su da tsofaffin da ke hannun su an kimshe a banki, ya haifar da gagarimar matsalar da ta kai har hasalallu na ƙona gine-gine har da bankuna.
Daga cikin abin da ya harzuƙa mutane su ka fara ɗaukar doka a hannun su, har da tinzirawar da CBN ya Yi masu, inda ya ce bankunan kasuwanci ne ke ɓoye sabbin kuɗaɗe ba su son bai wa kwastomomin su.
Rabuwar kawuna da saɓani tsakanin Shugaban Ƙasa da Gwamnoni ta yi tsamarin da har wasu sun garzaya Kotun Ƙoli sun maka shi kotu, su na neman kotu ta tilasta wa CBN ci gaba da karɓar tsoffin kuɗaɗe, tunda sabbin ba su wadata ba.
Babban abin tsaro dangane da wannan giribtu da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya yi na hana kuɗaɗe kewayawa a hannun ƙananan yan kasuwa da sauran masu sayen kayan buƙatun yau da kullum, wata illa ce wadda za a daɗe nan gaba ba a magance ta ba.
Tuni har an ma fara hasashen cewa an yi asarar kashi 3 bisa 100 na tattalin arzikin ƙasa a cikin ‘yan kwanakin nan. Kafin canjin kuwa har ana murnar cewa Najeriya za ta samu bunƙasar tattalin arzikin ƙasa da kashi 3.2 bisa 100 a 2023, kamar yadda Bankin Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya yi hasashe.
Abubuwa masu matuƙar hatsari da barazana sun faru kan tattalin arzikin Najeriya da ita kan ta zamantakewar ƙasar, waɗanda kuma barazana ce ga zaɓen 2023.
Idan za a iya tunawa, tun daga lokacin da Emefiele ya tsoma dungulmin yatsun sa cikin siyasa, wannan jarida ta fito ba sau ɗaya ba, ta yi kiran ya sauka daga shugabancin CBN, ko kuma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tsige shi. Kuma tun daga lokacin ne duk mai hangen nesa zai iya fahimtar cewa wannan ɗan ragabza da gidoga bai damu da da kiyaye dokokin aikin sa na shugabancin CBN ba, harankazamar sa kawai ya ke yi, duk kuwa da an san hakan babbar barazana ce ga ƙasar nan.
Saboda haka, Gwamnonin Najeriya sun yi gaskiya da su ka fito a ranar Lahadi su ka ce, “ƙwacen kuɗaɗe Emefiele ya yi wa jama’a, ba canji ko musayar kuɗaɗe ba.”
Tulin kuɗaɗen da ke zagayawa ana hada-hada da su a hannun jama’a, ba su ne ke kawo tsadar kayan masarufi, abinci da tsadar rayuwa ba. Abin da ke tsayar da tsadar farashi shi ne CBN ta gindaya ƙa’ida ko geji na canjin kuɗaɗen waje.
Idan aka kalli yadda masu tarzoma su ka riƙa ragargaza ginin bankuna su na gaggaɓe ƙofofin bankuna ko fasa na’urar ATM wurin neman a maido masu kuɗaɗen su a hannu, hakan ya isa a gane tsarin da Emefiele ya shigo da shi ba mai karɓuwa ko yin tasiri ba ne a cikin jama’a.
Rainin wayo da tunzira jama’a fa Emefiele ya yi, ya ce wai bankunan kasuwanci su ka ɓoye sabbin kuɗaɗe. Amma da ya sha matsa kamar gyaɗa, sai a fito ya faɗi gaskiya, ya ce ba a buga wadatattun sabbin kuɗaɗen da jama’a ke buƙata ba.
Idan aka dubi irin asarar rayuka da dukiyoyin da aka yi, sai kuma la’akari da halin ƙuncin da miliyoyin mutane ke ciki, babu sauran wata hujja ko dalilin da wani zai kawo domin ya kare wannan wawanci da Emefiele ya ɗibga.
Shin yanzu akwai wani maras kunyar da zai iya fitowa ya kare Emefiele ya ce bai cancanci a tsige shi ba? Tsige Emefiele shi ne alheri kuma yin hakan ne zai zama ruwan kashe dafin gubar da ya dasa a ƙasar nan.