Gwamna Ifeanyi Okowa na Delta, kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Atiku Abubakar a PDP, ya jajenta tare da yin ta’aziyya ga rundunar ‘yan sandan jihar da iyalan jami’an tsaron sa waɗanda ‘yan bindiga su ka bindige a Jihar Anambra.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Delta, Charles Aniagwu ne ya sanar da manema labarai haka a ranar Asabar a Asaba, babban birnin Jihar Delta.
Ya ce kwanton-ɓauna aka yi wa ‘yan sandan wajen ƙarfe 1:30 na rana a ranar Juma’a, aka bindige su kan hanyar Ihiala-Orlu zuwa Umuahia, a lokacin da su ke kan aikin su.
Ya ce waɗanda aka bindige ɗin sun haɗa Sufeto uku, wato Lucky Aleh, Celestine Nwadiokwu da kuma Jude Obuh, waɗanda ke aiki a Gidan Gwamnatin Delta a Asaba.
Ya ce za a yi rashi, jimami da kewar haziƙan jami’an tsaron waɗanda sun bayar da gagarimar gudummawa, wajen kawo zaman lafiya a jihar Delta.
Ya ce kisan na su dabbanci ne kuma ba za a lamunci irin haka ba a ƙasar nan, wadda ke ƙoƙarin ganin an ƙara samun haɗin kai a dunƙule domin tabbatuwar zaman lafiya da ci gaban al’umma.
“Haziƙan jami’an tsaron sun rasa rayukan su ne lokacin da suke kan hanyar tafiya yin gaba zuwa dama wurin kamfen ɗin PDP a jihar Abiya.
“Abin takaici, waɗannan ‘yan sandan sun saki hanyar da ta kamata su bi, su ka ɗauki wata hanya daban.
“An yi masu kwanton ɓauna ne a Ihiala-Orlu kan hanyar zuwa Umuahia, aka kashe uku a cikin su, amma ɗaya mai sanye da farin kaya ya tsallake.
“Mun gano gawarwakin su, kuma mun tuntuɓi iyalan su.”
Ya ce gwamnatin Delta ta yi jinkirin sanar da kisan na su, saboda ta na ta ƙoƙarin fara tuntuɓar iyalan mamatan tukunna.