Ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi ya lashe jihar Delta da ƙuri’u 341,866.
Delta ita ce jihar ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP, Gwamna Ifeanyi Okowa.
Tinubu na APC ya zo na biyu da ƙuri’u 161,600, sai Atiku Abubakar na PDP ya zo na uku da ƙuri’u 90,183.
A Jihar Ribas an ƙidaya ƙuri’un ƙananan hukumomi 21 daga cikin 23 na jihar.
Peter Obi ya samu 171,998, sai Tinubu 148,970, sai PDP kuma 84,994.
A jihar Ebonyi Peter Obi ya kwashi har 259,738, sai Tinubu 42,402, sai Atiku 13,503.
Discussion about this post