Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi zargin cewa an cukurkuɗa sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.
Obasanjo ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya sa sake bibiyar gaba ɗayan yadda aka tattara sakamakon zaɓen.
Haka Obasanjo ya bayyana a cikin wata wasiƙar da shi da kan sa ya sa wa hannu a ranar Litinin.
Ya yi zargin cewa “yawancin sakamakon zaben da aka tattara ba tare da na’urar tantance masu katin shaidar rajistar zaɓe (BVAS da rumbun Tattara Sakamakon Zaɓe (Server) ba, ba su nuna haƙiƙanin gaskiyar abin da ‘yan Najeriya su ka zaɓa ba.”
Obasanjo dai na ɗaya daga cikin masu goyon bayan jam’iyyar LP, wadda Peter Obi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.
PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa jam’iyyar LP da PDP da wasu ‘yan adawa sun fice daga Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe ta INEC a Abuja, a ranar Litinin.
Sun fice ne bayan sun zargi INEC da ƙin sakin sakamakon zaɓe a manhajar iREV.
Jam’iyyun sun ce ƙin fitar da sakamakon a iREV kamar yadda Dokar INEC ta tilasta a yi, ya nuna cewa akwai alamun zai yiwu a damalmala lissafin ƙuri’un.
A cikin sanarwar Obasanjo, ya jinjina wa Buhari a kan matsayin da ya ɗauka na tabbatar da cewa ya bar wa Najeriya gadon sahihin zaɓe.
Sai dai kuma ya yi kira ga Buhari ya ceto ƙasar nan daga hatsarin da ta ka iya faɗawa sakamakon zaɓe.
Haka a wani labarin, PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda PDP ta ƙi amincewa da sakamakon yawan ƙuri’un Peter Obi a Legas.
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ba ta amince da sakamakon yawan ƙuri’un da jam’iyyar LP ta Peter Obi ta samu a Jihar Legas ba.
Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Legas, Tunji Shelle wanda kuma shi ne ejan ɗin PDP wurin tattara sakamakon zabe a Yaba, Legas, ya ce “an yi ƙumbiya-ƙumbiya gabaɗayan aikin tattara ƙuri’un.”
“Ban amince da sakamakon zaɓen ba, kuma na ɗauki wannan matsaya ce a madadin jam’iyyar da na ke wakilta, PDP.” Haka Shelle ya bayyana wajen tattara sakamakon zaɓen a ranar Litinin.
“Ban amince da sakamakon da LP ta samu ba, ba wai don ba mu yi nasara ba. Amma saboda an saye waɗanda aka saye aka yi mana ƙumbiya-ƙumbiya.”
Peter Obi na LP dai ya lashe yawan ƙuri’un jihar Legas har 582,454, shi kuma Bola Tinubu na APC 572,606.
Atiku Abubakar na PDP ya samu 75,750.
“Ba na jin INEC ta bayar da kyakkyawan horon aikin zaɓe ga ma’aikatan wucin-gadin da ta ɗauka. Saboda a gaskiya ba mu shirya wa fara aiki da na’urar tantance masu rajistar zaɓe ba, wato BVAS. Saboda a wurin tantancewar ne ake yin amaja. Da yawan sakamakon zaɓen duk ba a ma loda su a BVAS ɗin. Amma haka aka fitar da sakamako.”
Ya ce kamata ya yi BVAS ya tsaftace aikin zaɓe, amma maimakon haka, sai ma ya ƙara maida hannun agogo baya.