Bayan ficewa daga zauren bayyana zabe da hukumar zabe ke yi a Abuja, jam’iyyun APC, NNPP da wasu 9 sun ce INEC ta yi watsi da korafin da wadannan jam’iyyu ke yi ta ci gaba da bayyana sakamakon zabe har sai ta kammala.
Idan ba a manta ba Jamiyya PDP da LP da wasu jam’iyyun sun fice daga zauren bayyana zabe a lokacin da PDP ta zargi hukumar da yin ba daidai ba a wajen bayyana zabe.
Jam’iyyun da ke mara wa NNPP da APC baya sun hada da A, AA, AAC, APM, NRM, YPP, ZLM, PRP and ZLP.
Shugaban hukumar Zabe ya ce ba za a dakatar da aikin bayyana sakamakon zabe ba duk da jam’iyyun sun bayyana korafin su cewa wai sai an fara sakin sakamakon zaben a rumbun tattara sakamakon zabe na hukumar a yanar gizo sannan a fara fadin sakamakon zaben.
Doka dai ta ba duk wanda bai gamsu da sakamakon zaben ya garzaya kotu domin kalubalantar haka.