Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa akwai wani tuggu da masu hana ruwa gudu a fadar shugaban kasa suke kitsawa don a samu matsala a zaben 2023, da zai kai ga a nada gwamnatin wucin gadi.
A hira da yayi da PREMIUM TIMES, El-Rufai ya ce wadannan mutane dake zagaye da Buhari sun kasa sun tsare lallai dole fa yadda suke so haka Buhari zai yi, kuma ba su nufin Najeriya da Alkhairi.
” Ba tsoron fadin sunayen su nake yi ba domin na san su. Babu abinda za su iya yi. Su ba mutane bane da ke da kima a idanun jama’a ba. Ba za su yi shiga siyasa a fafata da su ba domin ba za su Iya cin zabe ba a kasar nan. Abinda suke iya wa shine su boye bayan irin su Buhari suna sheke ayarsu babu mai ce musu komai.
El-Rufai ya ce shi ba mutum bane da zai ja bakin shi yayi shiru idan ya ga irin wadannan abubuwa, zai fito ya fallasa komai asan gaskiya komai dacin ta.
” Bari in gaya muku yau ku sani akwai wasu gaggan makusantan Buhari da suka nemi Kodai Ahmed Lawan, shugaban Majalisar dattawa ya zama dan takarar APC ko kuma Godwin Emefiele ya zama, kuma dukkan su sun wasa wukaken su dole sai daya daga cikin wadannan mutane biyu. Sai dai kash hakan su bai cimma ruwa ba.
” Tun daga wannan lokaci suka rika kitsa tuggu, makininita, sharri da bala’in dole sai an tarwatsa komai kowa ya rasa. To ba za mu barsu ba muma.