Kakakin Kamfen ɗin dan takarar shugaban kasa na PDP, Dino Melaye ya maida wa ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na APC, Kashim Shettima martani game da kalubalantar Atiku da yayi cewa ya faɗi mutum 8 da ya gina a zamanin da yake mataimakin shugaban kasa.
Idan ba a manta ba, Shettima ya ƙalubalanci Atiku da ya bayyana sunayen mutum 8 da ya gina a kasar nan, cewa in banda kasuwancin sa bai yi wa kowa komai ba a musamman yankin Arewa.
Sai dai kuma a wurin Kamfen ɗin PDP da aka yi a jihar Jigawa ranar Laraba, Atiku ya karyata haka in da ya lissafo wasu gaggan ƴan Najeriya da ya ce shi ya gina su suka kai matsayin da suke yanzu.
Dino ya ce na farko cikin wanda Atiku ya gina ya maida mutum shine Nasir El-Rufai gwamnan Kaduna na yanzu, sai kuma Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar EFCC da Sanata Danjima Goje, tsohon gwamnan jihar Gombe.
Sauran sun hada da, Ngozi Okonjo-Iweala, Jolly Nyame, Aisha Alhassan, Garba Shehu Kakakin Buhari, Charles Soludo, na Anambra, Usman Bugaji, Ben Obi da dai sauran su.
A wurin taron Atiku ya yai alkawarin farfaɗo da ayyukan noma a jihar da kuma sanar da tsaro a yankin baki daya.
Discussion about this post