Shugaban cocin ‘ Christ Embassy’ fasto Chris Oyakhilome ya bayyana cewa mala’ikan Allah ya nuna masa a wahayi dan takarar shugaban kasa da zai yi nasara a zaben 2023.
Oyakhilome ya fadi haka a sujadar da aka yi a cocin sa mai taken ‘Loveworld Praise-action’ da aka yi ranar Juma’ar makin jiya.
A bayanin da ya yi faston ya fadi sunayen ‘yan takarar shugaban kasa uku inda daga cikinsu ya ce Shugaban kasan Najeriya na cikin Littaffi Mai Tsarki, wato Bible.
Ya ce ‘yan takarar da Oyakhilome ya fadi sun hada da Bola Tinubu na jami’yyar APC, Atiku Abubakar na jami’yyar PDP sannan da Peter Obi na jami’yyar Labour Party LP.
Daya barawo ne, daya aljani, daya kuma waliyyi.
A bayanin da ya yi Oyakhilome ya ce dan takarar farko na da shekara 59 wanda ke tare da shaidan.
“Wannan mutumin baya cikin hankalinsa. Yana tare da shaidan wanda ke yi wa ‘yan Najeriya gori da dariya.
Ya ce dan takara na biyu barawo ne da zai ruguza kasar idan ya zama shugaban kasa.
“Idan har dan takarar na biyu ya ci zabe za mu rasa kasar mu domin zai siyar da kasan.
Sannan a dan takarar na uku ya ce duk da cewa sunan sa na Littafi Mai Tsarki yana fargaban ya yi nasaran a zabe amma baya so ya yi nasara.
Fasto a cikin bayanin sa, ya ce wanda zai yi nasara a zaɓen an ambaci sunan sa a wurare da dama a cikin Bible, da hakan ke nuna cewa ba dai Tinubu, ko Atiku bane, sai dai ko Peter Obi da daya ne daga cikin sahabban annabi Isa kamar yadda aka fadi a bible din.
Masu karatu sun yi sharhi akai.
Discussion about this post