Ofishin yada labarai na Kwamitin Kamfen din Bola Tinubu ya karyata raderadin da ake ta yadawa wai dan takarar ya jibge sabbin kudade don yin amfani da su lokacin zabe.
Babban mai ba dan takarar shawara kan harkokin yada labarai Mahmud Jega a wata takarda da ya saka wa hannu ranar litinin yace wannan labarin kanzon kurege ne kawai amma babu wani abu mai kama da haka.
Jega ya ce wannan labari ya samo asaline daga gungun wasu yan PdP da basu kaunar Tinubu da zaman lafiya a Kasar nan.
Bayan haka Jega ya karyata korafin wasu ‘yan jarida Jaafar Jaafar da Bulama Bukarta da ya zarge su da yi wa Tinubu Kazafin wai ta jibge miliyoyin nairori a fadin jihohin kasar nan domin siyan kuri’u lokacin zabe.
” Wannan kazafi ne karara da kuma cin mutuncin dan takarar shugaban Kasa na APC wanda Bulama Bukarta da Jafar Jafar da kowa ya sani suna yi wa PDP aiki ne suka yi masa. Sharri ce kawai da kuma bata sunan Tinubu amma babu gaskiya a abinda suka ce.
” Muna kira ga ‘yan Najeriya su yi watsi da irin wannan Kazafi da ‘yan koron PDP Bulama Bukarta da Jafar Jafar su ke yi don ganin bayan Tinubu, cewa shine zai yi nasara a zaben duk da sharri da suke kitsa masa.