Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Rab iu Kwankwaso ya karyata kalama Atiku Abubakar na PDP da ya ce wai yana tattaunawa da Kwankwaso game da yiwuwar yin ‘maja’ domin tunkarar zaben 2023.
A hira da Atiku yayi da BBC Hausa ya ce ba Kwankwaso ba har da Peter Obi na LP, duk suna tattaunawa domin ganin sun yi maja, su kada APC a zabe mai zuwa.
Sai dai kuma Kwankwaso ya karyata kalaman Atiku inda ya ce babu wani abu mai kama da haka da ke gudana a tsakanin jam’iyyun biyu.
” Rabon da inga Atiku ido da Ido tun a shekarar bara da muka hadu a hirar Talbijin. Amma tun daga wannan lokacin ban hada ido da shi ba ballantana ace wai muna wani tattaunawa.
“Ba mu tattaunawa da kowa, aii su Jam’iyyun PDP da APC suna ganin babu wanda ya isa su yi magana da shi, sun fi karfin yin haka. Mu ko yanzu muna so mu gaya wa yan Najeriya cewa idon mage ya waye yanzu, ba za mu tattauna da kowa ba.
” Idan ka ga mun zauna da wani shine fa idan zabe ya kai da sai an yi zabe zaga ye na biyu domin samun wanda yayi nasara. A nan ne za mu mu zauna da su domin mu tattauna. Ammam yanzu kowa tasa ta fishshe shi kawai.
Discussion about this post