A ƙoƙarin da gwamnatin sa ke yi na saisaita turbar tattalin arzikin ƙasa, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sakamakon tsarin sabunta kuɗaɗen da aka bijiro da shi, an samu nasarar raba mutane da naira tiriliyan 2.1, waɗanda ke hannayen su wasu ajiye a jibge ba tare da an kai su bankuna an ajiye ba.
Ya ce a shekarar 2015 lokacin da ya hau mulki, Naira tiriliyan 1.4 ce ke hannun mutane ana hada-hada ko ajiye da su.
Ya ce, “amma tsakanin 2015 zuwa 2022, yawan kuɗaɗen da ke hannun mutane ya ƙaru naira 3.23, a ciki kuma Naira biliyan 500 kacal ke cikin bankunan kasuwanci. Naira tiriliyan 2.7 kuma sun kasance dindindin a hannun jama’a.
Buhari ya ce wannan babbar matsala ta haifar da kasa yi wa tsadar rayuwa da farashin kayan ragama da linzamin yadda za a samu sa’ida da rahusa.
Ya ce tulin kuɗaɗen da ke hannun jama’a ya sa tattalin arzikin Najeriya ta kasa gaba, sai cikas ake ta fuskanta.
Buhari ya ce amma tsarin da aka shigo da shi a yanzu, an samu nasarar mayar da naira tiriliyan 2.1 zuwa banki.
Ya yi wannan bayani a jawabin da ya yi wa ‘yan Najeriya ranar Alhamis da safe, dangane da matsalar ƙarancin kuɗin da ake fuskanta.
Ana cikin wannan halin ne dai Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai (NBS), ta ce malejin tsadar rayuwa a Najeriya ya cilla sama da kashi 21.82% bisa 100%.
Yayin da miliyoyin ‘yan Najeriya ke fama da ƙarancin sabbin kuɗaɗe, malejin tsadar rayuwa ya cilla sama a cikin watan Janairu.
Tsadar rayuwa ya ƙaru zuwa 21.82, idan aka kwatanta da kashi 21.34 a cikin watan Disamba, 2022. Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ce ta bayyana haka a ranar Laraba.
Ƙididdigar ta nuna an samu ƙarin kashi 0.47 a cikin watan Janairu 2023.
‘Yan Najeriya sun shiga tarangahumar ƙuncin rayuwa biyo bayan sauya launin kuɗi da Gwamnatin Tarayya ta yi, amma kuma ta kasa wadatar da sabbin kuɗaɗen a hannun jama’a.
Wannan jarida ta buga labarin yadda wani jigon APC ya bayyana yadda jama’a ke rayuwar ƙunci sakamakon wannan sauyin launin kuɗi, inda har ya ragargaji Buhari da yin kunnen-uwar-shegu da ƙorafe-ƙorafe da koke-koken da jama’a ke yi.
Har cewa ya yi sai fa ‘yan Najeriya sun miƙe Buhari ya ga tsawon su, sannan zai gane da gaske su ke yi
Mataimakin Daraktan Kamfen na zaɓen shugaban ƙasa na APC, a ɓangaren bunƙasa kayan noma na sayarwa, Retson Tedheke, ya ce ƙarancin sabbin kuɗi da ake fama da su sanadiyyar canjin kuɗin da Shugaba Buhari da Gwamnan CBN Godwin Emefiele su ka ƙaƙaba, ya na ci gaba da kashe harkokin kasuwanci a yankunan karkara.
Ya ce lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su ƙalubalanci Buhari tunda dai ya toshe kunnen sa biyu daga sauraren koke-koke da ƙorafe-ƙorafen jama’a.
A cikin wani bidiyon da ya watsa a shafin sa na Tiwita a ranar Talata, Tedheke ya ce Buhari ya na azabtar da al’ummar cikin karkara. Ya ce a yanzu masu aikin kayan gona ba su iya sallamar ma yi masu aikin gona ko leburanci.
“Duk inda ka shiga a ƙauyuka, mutane ne za ka gani su na mutuwa saboda yunwa, ga kuma azabtarwar da su ke sha a ƙarƙashin Buhari wanda ke kiran kan sa shugaban ƙasa, shugaban talakawa. Ya wannan mutumin wai zai ƙirƙiro tsarin da zai riƙa kashe manoma a yankunan karkara?!
“Ni manomi ne, mu na noma a inda mutane kusan 500 ke mana aiki, amma ba mu iya biyan su haƙƙin su. Saboda mafiyawan su ba su da asusun ajiya a banki.
“Ki dai Shugaban Ƙasa kurma ne, ba ya jin magana ne. Lokaci ya yi da ‘yan Najeriya da za su dubi tsabar idon shugaban ƙasa su ce masa, ‘kai malam, mu fa mu ka zaɓe ka, kuma mulkin dimokraɗiyya ke yi, ehe.’
“Su fito su ce masa yanzu fa tsarin mulki ne ake yi wanda abin da ‘yan Najeriya su ka fi so shi ne za a yi masu.
“Idan Majalisar Zartaswa ba ta iya faɗa maka ka ji, dattawa ma ba ka jin maganar su, ba ka jin maganar talakawa, ba su ma iya yi maka maganar. Gwamnoni ba su iya yi maka magana, to shin kai wane ne?
“Kai wane ne da har ‘yan Najeriya ba su iya yi maka magana? Lafiyar ka ƙalau kuwa?”
Ya ce a yanzu kires ɗin ƙwai na naira N1,800 ya dawo ya na sayar da shi naira N1,300.00.