Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya maida wa gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai martani cewa babu wani dan takara da Buhari yake mara wa baya a zaben 2023.
” Buhari ya yi alakwarin za a yi zabe ne kamar yadda doka ta ce, kuma baya goyon bayan kowani dan takara, wanda ya ci shi za a ba. Hakan kuma sune furucin Buhari a ko da yaushe. Ko a Daura sai da ya maimaita haka cewa baya goyon bayan ko wani dan takara.
Wannan martani ya biyo bayan kalaman da El-Rufai yayi ne a hira da yayi da talbijin din Channels ranar Talata inda ya ke zargin akwai wadanda suke yi wa takarar Bola Tinubu na APC zagon kasa.
El-Rufai ya ce : Babu alfanun da canjin kudi zai yi wa kasa a dan kankanin lokaci irin haka da zabe ya karato da dole sai an yi su. Sannan kuma matsalolin wahalar mai da ake fama da shi da gangar aka kirkiro shi domin a kawai mutane su yi wa jam’iyyar bore, su ki zabar ta a zabe mai zuwa.
” Nan ni da kai na tare da wasu gwamnoni muka je fadar shugaban kasa muka ba shi shawarwain yadda za a kawo karshen matsalar mai, kuma har kudirori muka aika majalisa akai amma shiru, sannan kuma wadanda ke da ikon tabbatar da abin ba a hukunta su ba.
” Maganar sauya launin kudi kuwa, babu wani alfanu da sauya kudi zai yi wa Najeria a wannan dan kankanin lokaci, kuma wai sai da aka tunkari zaben kasa sannan ace wai za a bijiro da irin wannan abu haka. Tsakani da Allah dole talaka ya fusata ya yi wa jam’iyyar Bore ba.
El-Rufai ya ce a daina ganin laifin Emefiele kan sauya launin kudin kasa, idan ba a manta ba shima shugaba Buhari na da tarihin sauya launin kudi ba tun yanzu ba don bankado masu harkalla.