Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ƙaryata rahotannin da aka buga, inda aka ce Gwamnan CBN Godwin Emefiele ya ce rashin takardun buga kuɗi ne ya haifar da ƙarancin sabbin kuɗi a faɗin ƙasar nan.
“Mu na so mu fito ɓaro-ɓaro mu sanar da cewa babu inda Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya furta wa Majalisar Jihohin Najeriya cewa rashin wadatar takardun buga kuɗi ne ya haifar da ƙarancin sabbin kuɗi a ƙasar nan, a taron da suka yi da shi na ranar Juma’a.”
Kakakin Yaɗa Labaran CBN Osita Nwasinobi ne ya bayyana wancan raddi na sama, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
Ya ce Emefiele ya shaida wa majalisar cewa Kamfanin Buga Kuɗi na Najeriya ya na aiki kan buga sabbin kuɗaɗen da ‘yan Najeriya za su ci gaba da hada-hada da su.
“CBN ya gode da irin damuwar da ‘yan Najeriya da sauran cibiyoyin hada-hada ke nunawa kan samar da sabbin kuɗi.
Sai dai kuma sanarwar ta ce CBN ya damu kuma ya razana sosai ganin yadda wasu masu mugun nufi ke ƙoƙarin kitsa tuggun haɗa jama’a rikici da bankin da kuma goga masa baƙin jini a idon ‘yan Najeriya.
“Mu na sanar da cewa Kamfanin Buga Kuɗi na Najeriya ya na da wadatattun takardun da zai buga sabbin kuɗaɗe da su, yadda za su wadaci ƙasar nan daidai yadda ake buƙata.”
Sanarwar ta nesanta CBN da mallakar wata murya da ake watsawa a soshiyal midiya, ana cewa CBN na shirin rufe wasu bankuna da ke ɓangaren wani yankin ƙasar nan.
Discussion about this post