Kotun Koli a Abuja ta yanke hukuncin taƙaddamar da ake ta yi tsakanin ƴan takarar kujerar sanatan Kaduna ta Tsakiya, takanin Lawal Adamu, Mr La da Ibrahim Usman Sardaunan Badarawa, da yaki ci yaki cinyewa.
Duka alkalai biyar da suka yi zaman yanke hukuncin sun amince cewa Lawal Adamu Mr La ne dan takarar sanatan Kaduna ta tsakiya kamar yadda kotun daukaka kara ta yanke a baya.
Idan ba a manta ba Ibrahim Usman Sardauna Badara ya garzaya Kotun Koli yana kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara da ta bayyana Mr La dan takarar sanatan Kaduna ta Tsakiya.
Sai dai kuma hakar sa bai cimma ruwa ba domin duka alkalai 5 sun tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara cewa Lawal Adamu Mr La ne dan takarar kujerar.
Discussion about this post