Mataimakin Daraktan Kamfen na zaɓen shugaban ƙasa na APC, a ɓangaren bunƙasa kayan noma na sayarwa, Retson Tedheke, ya ce ƙarancin sabbin kuɗi da ake fama da su sanadiyyar canjin kuɗin da Shugaba Buhari da Gwamnan CBN Godwin Emefiele su ka ƙaƙaba, ya na ci gaba da kashe harkokin kasuwanci a yankunan karkara.
Ya ce lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su ƙalubalanci Buhari tunda dai ya toshe kunnen sa biyu daga sauraren koke-koke da ƙorafe-ƙorafen jama’a.
A cikin wani bidiyon da ya watsa a shafin sa na Tiwita a ranar Talata, Tedheke ya ce Buhari ya na azabtar da al’ummar cikin karkara. Ya ce a yanzu masu aikin kayan gona ba su iya sallamar ma yi masu aikin gona ko leburanci.
“Duk inda ka shiga a ƙauyuka, mutane ne za ka gani su na mutuwa saboda yunwa, ga kuma azabtarwar da su ke sha a ƙarƙashin Buhari wanda ke kiran kan sa shugaban ƙasa, shugaban talakawa. Ya wannan mutumin wai zai ƙirƙiro tsarin da zai riƙa kashe manoma a yankunan karkara?!
“Ni manomi ne, mu na noma a inda mutane kusan 500 ke mana aiki, amma ba mu iya biyan su haƙƙin su. Saboda mafiyawan su ba su da asusun ajiya a banki.
“Ki dai Shugaban Ƙasa kurma ne, ba ya jin magana ne. Lokaci ya yi da ‘yan Najeriya da za su dubi tsabar idon shugaban ƙasa su ce masa, ‘kai malam, mu fa mu ka zaɓe ka, kuma mulkin dimokraɗiyya ke yi, ehe.’
“Su fito su ce masa yanzu fa tsarin mulki ne ake yi wanda abin da ‘yan Najeriya su ka fi so shi ne za a yi masu.
“Idan Majalisar Zartaswa ba ta iya faɗa maka ka ji, dattawa ma ba ka jin maganar su, ba ka jin maganar talakawa, ba su ma iya yi maka maganar. Gwamnoni ba su iya yi maka magana, to shin kai wane ne?
“Kai wane ne da har ‘yan Najeriya ba su iya yi maka magana? Lafiyar ka ƙalau kuwa?”
Ya ce a yanzu kires ɗin ƙwai na naira N1,800 ya dawo ya na sayar da shi naira N1,300.00.