Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya roƙi ƴan Najeriya su yi hakuri su ci gaba da bin dogayen layi a bankuna don ƙarabar sabbin kudi, yana mai cewa nan ba da daɗewa ba, komai zai koma yadda ya ke a da.
Mutanen Najeriya na fama da wahalar ƙarancin sabbin kuɗi a faɗin kasar tun bayan cikar wa’adin watanni uku da gwamnati ta saka na kowa ya canja tsoffin takardun kuɗin sa zuwa sabbi.
Mutane kan yi cincirindo da bin dogon layi a harabar bankuna da wuraren cire kuɗi na ATM domin su samu sabbin kuɗin.
Emefiele ya bayyana wa mutane a garin Legas cewa nan ba da daɗewa ba kudin zai wadatu ko ina kowa ya samu.
” Hakuri za ku yi ku rika wa bankuna sammako kuna shiga layin cire kuɗi. Ida suka kare, sai kara yin asubanci washe gari ku dawo har ku samu. A haka za a samu kuɗin kuma a hankali komai zai wanye.
” Bayan haka mun umarci bankuna su kafa rumfuna su e ka baiwa mutane lamba, idan aka kira ka sai ka shiga banki ka karbi kudi. Idan kudi ya kare sai ka dawo gobe a ci gaba daga inda aka tsaya jiya.
A karshe Emefiele ya ce a hankali komai zai wanye harkokin kasuwanci su koma kamar yadda suke baya.