A ranar Laraba ce Kotu Ƙoli ta bayyana cewa za ta yanke hukunci a ranar 6 Ga Fabrairu domin bayyana wanda ya cancanta ya tsaya wa APC takarar sanatan Shiyyar Yobe ta Tsakiya, tsakanin Bashir Machina, ɗan takarar da ya ci zaɓen fidda-gwani da kuma Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan.
Ahmad Lawan shi ne ke zaune kan kujerar sanata ɗin, to amma sai Machina ya kayar da shi a zaɓen fidda gwanin da aka yi cikin 2022.
Cikin Nuwamba 2022 ne Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja ta ƙara tabbatar wa Machina halascin takarar sa ta sanata a zaɓen 2023.
Yayin da Lawan ya ce ya haƙura ba zai kai ƙara a Kotun Ƙoli ba, ita kuwa APC cewa ta yi ba ta haƙura ba, sai ta garzaya Kotun Ƙoli ɗin ta kai ƙara.
APC ta yi tsayuwar daka cewa Ahmad Lawan ne halastaccen ɗan takarar ta, duk kuwa da cewa bai shiga takarar zaɓen fidda gwanin sanata a ranar da aka yi zaɓen ba. Sanata Lawan ya na can a lokacin ya na neman takarar zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa a APC.
Hujjojjn Lauyan APC, Mai Goyon Bayan Sanata Lawan:
A ranar Laraba lauyan APC mai suna Sepribo Peters ya yi tankiyar cewa zaɓen fidda gwanin da aka gudanar a ranar 28 Ga Mayu, 2022, wanda ya bai wa Machina nasara, to zaɓen ya karya ƙa’idar Dokar Zaɓe ta Ƙasa.
Lauyan ya ce Ɗanjuma Manga wanda gudanar da zaɓen fidda gwanin, ba Kwamitin Zartaswar APC ne ya naɗa shi aikin gudanar da zaɓen ba.
Ya shaida wa Alƙalan Kotun Ƙoli su biyar a ƙarƙashin jagorancin Centus Nweze cewa APC ta soke zaɓen fidda gwanin da Bashir Machina ya yi nasara, saboda jam’iyyyar ta lura an yi ba daidai ba da kauce ƙa’ida yayin zaɓen.
“Kamata ya yi a ce a ranar 27 Ga Mayu aka yi zaɓen, ba 28 ga Mayu ba.” Cewar Peters, lauyan APC.
Ya ce zaɓe na biyu da aka gudanar ranar 9 Ga Mayu, 2022, Kwamitin Zartaswar APC ne ya gudanar da shi, kuma Sanata Ahmad Lawan ya yi nasara.
A kan haka sai Peters ya roƙi Kotun Ƙoli ta ayyana Sanata Lawan a matsayin ɗan takarar Sanatan Shiyyar Yobe ta Arewa, na jam’iyyar APC.
Hujjojin Lauyan Bashir Machina:
Sarafa Yusuf lauyan Bashir Machina, ya ragargaji hujjojin lauyan APC da cewa bai ma san abin da ya ke yi ba.
“Da farko dai APC ba ta ƙalubalanci hukuncin Babbar Kotu ba da hukuncin Babbar Kotun Tarayya, waɗanda su ka bai wa Machina nasara.”
Ya ce Manga wanda ya gudanar da zaɓen fidda gwanin da Bashir Machina ya Yi nasara, mamba ne na Kwamitin Zartaswar APC, kuma kwamitin ne aka ɗora wa nauyin gudanar da zaɓen fidda gwani.
Bayan Kotun Ƙoli ta saurari bayanan lauyoyin ɓangarorin biyu, an aza ranar 6 Ga Fabrairu cewa a ranar za a yanke hukunci, a bai wa mai rabo rabon sa.
Sai dai kuma Alƙalai uku na Kotu Ɗaukaka Ƙara a ƙarƙashin jagorancin Monica Dongban-Mensem, wadda ita ce Shugabar Alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙara, ta ce ɗaukaka ƙarar da aka yi raini ne ga tsarin kotu.
Dongban-Mensem ta ce Babbar Kotun Tarayya