Kotun majistare dake Kafanchan jihar Kaduna ta tsare wani magidanci mai suna Augustine Luka a kurkuku bisa laifin yi wa matarsa barazanar kisa.
Hukumar NSCDC ta kama Luka bisa laifuka da suka hada da cin zarafi da hana jami’in gwamnati gudanar da aikin sa.
Jami’in tsaron da ya kawo kara Marcus Audu ya ce rundunar ta kama Luka bayan karar da aka kawo hukumar ranar 8 ga Fabrairu.
Audu ya ce matar Luka, Hassana Augustine ta koka kan yawan yi mata barazanar kisa da luka ya ke yi a duk lokacin ya yayi mata shegen duka.
Ya ce Hassana ta kai kukanta ga Iyayen mijinta amma ko da suka aika ya zo domin a sassanta su Luka ya ki zuwa.
Audu ya ce da Hassana ta ga cewa matsalar ta ki ci ta ki cinyewa sai ta kai karar Luka cibiyar sauraron kararrakin cin zarafin mata da yara ‘ Salama Sexual Assault Referral’ domin su shiga cikin maganar.
Ya ce cibiyar ta aika wa Luka wasikar sammaci amma ya ki zuwa sannan ya lakadawa Hassana dukan tsiya saboda kai karar sa da ta yi.
Bayan haka Luka ya je cibiyar inda ya nemi lakawa wa manajan cibiyar duka sai dai kafin ya aikata hakan ne jami’an tsaron dake wurin suka kama shi sannan suka damka shi hannun rundunar NSCDC.
A kotun Luka ya musanta duk laifukan da ake zarginsa da su.
Alkalin kotun Michael Bawa ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 7 ga Maris.