Babbar Kotun Jihar Kogi ta bayar da umarnin a kama Shugaban EFCC a tsare shi a kurkuku, saboda ya keta alfarmar kotu.
Sannan kuma kotun ta umarci Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya ya sa a kama Abdulrasheed Bawa, a tsare shi kwanaki 14 a kurkuku, saboda ya aikata laifin ƙin bin umarnin kotu.
Mai Shari’a Ruƙayat Ayoola ce ta yanke wannan hukunci na umarnin a tsare Bawa a kurkuku, “har sai ya wanke kan sa daga saɓa umarnin kotun da ya yi.”
Shugaban EFCC dai ba ya kotun a lokacin da aka yanke hukuncin, sai dai kuma ba a jin za a iya kama shi ɗin har a garƙame shi a kurkuku, idan aka yi la’akari da ire-iren waɗannan umarni da kotuna daban-daban su ka bayar a kan sa a baya.
Ayoola ta bada umarnin a damƙe Bawa, biyo bayan da wani mai suna Ali Bello ya nemi kotun ta kama shi, bisa zargin ya yi fatali da umarnin kotu a ranar 15 Ga Disamba, 2022, bayan kuma tun a ranar 12 ga Disamba ɗin ma akwai irin wannan umarnin a kan sa.
A ranar 12 ga Disamba, 2022 ce kotun ta yanke hukuncin cewa kamun da EFCC ta yi wa Bello na ranar 29 Ga Nuwamba, 2022 ya saɓa doka, saboda babu sammacin kamun sa daga kotu, kuma ba a shaida masa laifin da ya aikata ba.
A kan haka ne kotun ta ce kamun da EFCC ta yi wa Aliyu Bello ya danne masa ‘yancin walwala, wanda Dokar Najeriya da Kundin ‘Yancin Bil’Adama na Afrika ta ba shi.
Kotu ta nemi Bawa ya buga wasiƙar neman afuwar Bello a wasu jaridun Najeriya, sannan kuma ya biya shi diyyar naira miliyan 10.