Babbar Kotun Tarayya ta karɓi riƙon da Festus Keyamo ya yi mata na gabatar da sabbin zarge-zargen harƙalla kan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Keyamo wanda lauya ne, Ƙaramin Ministan Ƙwadago kuma Daraktan Yaɗa Labaran Rundunar Kamfen ɗin Bola Tinubu na APC.
Ya na so jami’an tsaro su kama Atiku tare da gurfanar da shi kotu kan zargin harƙallar maƙudan kuɗaɗe.
A ranar 1 Ga Fabrairu ne Mai Shari’a James Omotosho ya amshi buƙatar Keyamo, inda ya amince masa ya gabatar da takardun bayanan sammacin da ya nema.
Cikin kwafen bayanan da PREMIUM TIMES ta samu a ranar Juma’a, Omotosho, ya bada iznin a aika da sammacin kwafen zarge-zargen ga ko da mutum ɗaya ne tal da aka gani a Hedikwatar Kamfen ɗin Atiku Abubakar, wadda ke kan titin Ademola Adetokunbo, Wuse 2, Abuja.
Mai Shari’a ya ce idan ma ba a ga ko da mutum ɗaya ba, to za a iya liƙa kwafen takardun sammacin a jikin bangon ginin ofishin kamfen ɗin Atiku.
Sai dai kuma Omotosho ya ɗage sauraren batun shigar da ƙarar har sai ranar 7 Ga Maris, mako ɗaya bayan zaɓen shugaban ƙasa kenan.
Idan ba a manta ba, a ranar 16 Ga Janairu Keyamo ya bai wa hukumar CCB wa’adin sa’o’i 72 ta kama ita da ICPC da EFCC su kama Atiku Abubakar bisa zargin harƙalla.
Bayan cikar wa’adin ne da Keyamo ya ba CCB, ICPC da EFCC ba su kama Atiku ba, sai ya garzaya kotu.
Keyamo ya kafa dalilin maka Atiku ƙara ne daga bayanan da wani tsohon hadimin Atiku mai suna Micheal Achimugwu ya riƙa yi, ya na iƙirarin harƙallar da ya ce Atiku ya riƙa yi lokacin da ya ke Mataimakin Shugaban Ƙasa.