Shugaban PDP na FCT Abuja, Sunday Zaka ya rasa ran sa, sanadiyyar hatsarin motar da ya ritsa shi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Zaka ya rasa ran sa yankin Abuja, cikin talatainin daren Juma’a, kusa ga wayewar garin Asabar ranar zaɓe.
Wani hadimin sa mai suna Bawa Benjamin, ya tabbatar wa jaridar cewa hatsarin ya faru ne wajen ƙarfe biyu na dare, kan hanyar Guda zuwa Arena, a Kuje.
Ya ce mamacin ya rasa ran sa bayan motar da ya ke tuƙawa ta ƙwace ta kai wa bishiya karo, kan hanyar sa ta komawa gida daga taron siyasa wanda ya kai su har tsakiyar dare a Abuja.
Benjamin ya ce an garzaya da mamacin Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada, inda likitoci su ka tabbatar da rasuwar sa.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Kuje, Abdullahi Suleiman Sabo, ya tabbatar da rasuwar shugaban na PDP reshen FCT Abuja.