A ranar Juma’a ce kamfanin NNPCL ya kammala mallake dukkan kadarorin NNPC mallakar gwamnatin tarayya, bayan shafe shekaru 46 gwamnati na tafiyar da hukumar kamfanin fetur ɗin na NNPC.
An dai gudanar da ƙwarya-ƙwaryan bukin damƙa haƙƙin mallakar NNPC ɗin a hannun NNPCL, a Hedikwatar NNPC da ke Abuja, a ranar Juma’a.
Idan ba a manta ba, cikin watan Yuli 2022 ne Buhari ya ƙaddamar da sabon kamfanin NNPCL, lamarin da ya maida NNPCL a hannun ‘yan kasuwar da su ka zuba hannayen jarin su a kamfanin, ita kuma gwamnatin tarayya ta cire hannun ta daga haƙƙin ciyarwa da shayar da kamfanin.
An dai mayar da NNPC a hannun ‘yan kasuwa bayan da Shugaban Ƙasa ya sa wa Sabuwar Dokar Fetur (PIA) hannu cikin Satumba, 2021.
Sai dai kuma an damƙa NNPC ɗin a hannun NNPCL, a daidai lokacin da Najeriya ke fama da ƙarancin fetur da kuma tsadar sa.
Sannan kuma babbar matsala a yanzu ita ce yadda za a iya warware ƙaƙudubar kuɗaɗen tallafin fetur.
Domin ko a cikin makon jiya sai da Shugaban NNPCL, Mele Kyari ya yi kukan cewa Najeriya na asarar naira 202 a kowace litar fetur ɗaya, naira biliyan 400 kenan a wata – Kyari
Shugaban NNPCL Mele Kyari ya ce a duk wata Najeriya ta na kashe fiye da naira biliyan 400 wajen biyan kuɗin tallafin fetur.
Kyari ya ce tuni NNPCL ce kaɗai ke sayo fetur daga waje tsawon shekaru, kuma NNPCL ɗin ne ke jin jikin biyan ɗoriyar maƙudan kuɗaɗe da sunan cike giɓin tallafin fetur.
Ya ce sauran kamfanoni sun daina shigo da fetur saboda wahalar da suke fuskanta kafin samun canjin dalilin Amurka da za su buƙata kafin su sayo fetur ɗin a waje.
“Har a kwanaki uku da su ka gabata, idan NNPLC ya sayo fetur a waje, to duk lita ɗaya ta na tashi a kan N315 daga cinikin sa, lodin sa, ɗauko shi zuwa sauke shi. Mu kuma mu sakar wa kwastomomin mu kan naira 113. Kenan akwai bambancin naira 202 a kowace lita kenan mu ka shigo da ita cikin ƙasar nan.
“Idan aka lissafa asarar kuɗin tallafin lita ɗaya naira 202 sau lita miliyan 66.5, sannan a yi sau 30 na kwanan wata, to za a ga a duk wata ana asarar biyan naira biliyan 400 kenan.”
Kyari ya ce duk da kuɗin tallafi na cikin kasafin kuɗi, amma haka NNPCL ke ci gaba da biyan kuɗaɗen ba tare da Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe da Kasafi na biyan ta abin da ya ke kashewa ba.
Kyari ya ce NNPCL na fuskantar matsanancin ƙalubalen rashin tara kuɗaɗen shiga, saboda waɗanda ta ke tarawa ɗin su na tafiya wajen cike giɓin tallafin fetur, alhali kuma Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe ba ta biyan NNPCL abin da ya ke kashewa duk wata.