Ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi ya samu ƙuri’u 132 a rumfar zaɓen Abdullahi Adamu, Shugaban APC na ƙasa, a mazaɓar sa a Jihar Nasarawa.
APC mai Bola Tinubu ya samu 85 ya zo na biyu, a zaɓen wanda aka yi a Rumfar Zaɓe ta Angwarimi Ward, GRA, A1-PB da ke Keffi, Jihar Nasarawa.
Haka APC da Adamu duk sha ragargazar tsiya a zaɓen sanata da na ɗan majalisar tarayya.
Jam’iyyar SDP ce ta yi wa APC kwankwatsa a zaɓukan Sanata da na Majalisar Tarayya. SDP ta samu 184, LP 42, PDP 22 a zaɓen Sanata.
A zaɓen Majalisar Tarayya kuma APC ta zo ta biyu da ƙuri’u 46, SPD da 158 sai PDP da ƙuri’u 41.
A Abuja can a Fadar Shugaban Ƙasa kuwa, Jam’iyyar Peter Obi ta ragargaji su O’o da O’o a rumfunan zaɓen kewayen Fadar Shugaban Ƙasa
Jam’iyyar LP wadda Peter Obi ke takarar shugaban ƙasa, ta lashe zaɓen rumfar zaɓe ta 12 da ke Fadar Shugaban Ƙasa, amma dai wannan jaridar ba ta kai ga samun sauran sakamakon zaɓen ba tukunna.
Peter Obi ya lashe yawancin rumfunan zaɓen kewaye da fadar ta Shugaban Ƙasa a Abuja.
Runfa mai lamba 022, Obi ya samu ƙuri’u 174, PDP 78, APC kuma 71.
Runfa mai lamba 021 kuwa Obi na LP ya samu 190, APC 87, PDP 70.
A lamba ta PU130 kuwa, LP ta samu 113, APC 26 PDP 25.