Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya sha kaye a takarar zaɓen sanatan da ya tsaya.
Tsohon ɗan aiken sa ne Titus Zam ya kayar da shi a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Zam tsohon Mashawarcin Gwamna ne a fannin Ƙananan Hukumomi da Masarautun Gargajiya ga Samuel Ortom.
Lokacin da Ortom ya fice daga APC ya koma PDP, Zam sai ya yi zaman sa bai canja sheƙa ya bi gwamnan ba a cikin 2018.
Zam dai ɗan ga-ni-kashe-nin George Akume ne, wanda a yanzu shi ne Ƙaramin Ministan Ayyukan Musanman da Harkokin Gwamnatin Tarayya, Jihohi da Ƙananan Hukumomi.
Ya samu ƙuri’u 143,151, Ortom kuma ya samu 106,882, sai Mike Gbillah na LP ya samu 51,950.
Aƙalla dai gwamnonin da ke kan mulki bakwai ne su ka shiga takarar sanata amma su ka faɗi.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda guguwa ta tarwatsa garken wasu gwamnonin da su ka shiga takarar sanata.
Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Enugu ya sha ƙasa a takarar Sanatan Enugu ta Arewa da ya fito a ƙarƙashin PDP.
Ɗan takarar LP Okechukwu Ezea ne ya kayar da shi.
Ƙoƙarin Ugwuanyi na tafiya Majalisar Dattawa bayan kammala wa’adin mulkin shekara takwas bai yi nasara ba.
Ɗan takarar LP ya samu ƙuri’u 104,492, shi kuma Gwamna Ugwuanyi ya tashi da 46,948, bai ma kai rabin wanda ya kayar da shi ba kenan.
Shi kuwa ɗan takarar APC Ejike Eze ƙuri’u 6,816 kaɗai ya samu.
Irin yadda aka yi wa Ugwuanyi na Enugu, haka shi ma Ben Ayade ma Cross River ya sha kaye a hannun Sanatan da ke kan kujera a yanzu, Jarigbe Agom-Jarigbe.
Ayade Gwamnan APC ya sha kaye a hannun Jarigbe ɗan PDP, wanda ya lashe ƙuri’u 76,145, shi kuwa Ayade aka bar shi da 56,595.