‘Yan bangar siyasa da aka fi sani da ‘yan jagaliya, sun hargitsa rumfunan zaɓe a jihohi biyu, tare da sace na’urorin tantance masu rajistar zaɓe (BVAS) guda takwas.
Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ne, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka, sa’o’i kaɗan bayan fara zaɓen shugaban ƙasa yau Asabar a faɗin ƙasar nan.
Ya bayyana haka ne lokacin da ya ke wa manema labari bayanan yadda zaɓe ke gudana a faɗin ƙasar nan.
Ya ce amma tuni an ci gaba da gudanar da zaɓe a rumfunan biyu yayin da aka kai wa jami’an zaɓen wasu ‘safayar’ na’urorin BVAS.
Ya ce an ɗan samu tsaikon fara zaɓe da wuri a wani yanki na Jihar Neja, sakamakon harin da ‘yan bindiga su ka kai wa yankin.
Ya kuma yarda an samu lattin isar kayan zaɓe da jami’an zaɓe a mazaɓu da dama.
Ya ce ba za a bar duk wanda BVAS bai tantance shi ba yin zaɓe.
A wani labarin kuma, ‘yan iskan gari ne su ka afka wa jami’an zaɓe da sara a Gombe.
Wasu ‘yan iskan gari sun kai farmaki ofishin Hukumar Zaɓe (INEC), inda su ka banka wa ofishin wuta, kuma su ka ji wa wasu jami’an zaɓe na wucin-gadi rauni.
Lamarin ya faru a sansanin ma’aikatan zaɓe da ke Firamaren Tudunwada, ciki garin Gombe.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Gombe, Mahid Abubakar ya tabbatar da faruwar farmakin ga wakilin PREMIUM TIMES.
Maharan sun ji wa jami’an zaɓe uku rauni sakamakon sara da su ka yi masu da adduna. Su ukun dai an garzaya da su asibiti ana kula da su.
Wani daga cikin ma’aikatan wucin gadin wanda lamarin ya ritsa da su, ya shaida wa wakilin mu ce maharan sun ƙwace wayoyin hannu uku, ‘power bank’ da dama da wasu kayayyaki.
Ya ce waɗanda su ka ji ciwo wurin ƙoƙarin gudun tsira su na da yawan gaske.
“An nemi jami’an ‘yan sandan da ke gadin wurin da mai gadin makarantar domin su kai ceto, amma ba a gan su ba. Cikin wayoyin da aka ƙwace har da na abokai na. Ni ma na ji ciwo yayin gudu.”
Ya ce an kai masu harin ne wajen ƙarfe 11 na dare.
Sai dai ba a san yadda wannan hari zai shafi aikin zaɓe a mazaɓar ko a rumfar zaɓen ba.
Discussion about this post