Uwar jam’iyyar APC ta Jihar Adamawa ta yi fatali da dakatarwar da reshen jam’iyyar na mazaɓar ƙaramar hukuma ya yi wa Aishatu Binani, ‘yar takarar gwamna ta APC a jihar.
A ranar Juma’a ce dai wata sanarwa ta fito wadda aka danganta da shugabannin APC na Ƙaramar Hukumar Yola ta Kudu, mazaɓar Binani, inda su ka ce sun dakatar da ita tsawon watanni shida, sadoda nuna rashin biyayya ga wasu jiga-jigan jam’iyya da kuma ƙin bin umarnin Kotun Ɗauka Ƙara da Binani ta yi.
Sai dai kuma uwar jam’iyya ta Jihar Adamawa ta yi fatali da dakatarwar, tare da hakan da aka yi wa ‘yar takarar haramtacciyar dakatarwa ce, ta an saɓa wa dokar Najeriya.
“Mu na sanar da cewa mu uwar jam’iyyar APC a Jihar Adamawa ba mu amince da dakatarwar da aka ce wai an yi wa ‘yar takarar gwamnan jiha, Aishatu Binani a mazaɓar Adamawa ta Kudu ba.
“Dakatarwar ta saɓa da dokar ƙasa, haramtacciya ce, kuma ba ta dakatu ɗin ba. Rashin tunani ne, neman raba kan jam’iyya ne kuma babu wani dalilin da zai tilasta a yi haka.”
Haka dai wata sanarwa kuma raddi ya ƙunsa, wanda Sakataren APC na Jihar Adamawa, Raymond Chidama ya fitar kuma ya sa wa hannu.
Mu na kira ga dukkan wani ɗan jam’iyya mai biyayya ya nisanci wannan sanarwar dakatarwar da aka ce wai an yi wa Binani.”
Zagin Da Ake Wa Binani:
Shugabannin APC na Ƙaramar Hukuma sun nemi Binani ta bayyana domin kare kan ta daga zargin da wani Auwal Bawuro ya rubuta ya na yi mata. Bawuro ɗan jam’iyyyar APC ne.
“Ana zargin ta da yin fatali da masu ruwa da tsaki na APC a Ƙaramar Hukumar Yola ta Kudu da kuma kin bin umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara.
A kan haka ne aka bada sanarwar dakatar da ita tsawon watanni shida.
An bayyana dakatarwar saura kwanaki 11 kacal a yi zaɓen gwamna, wanda Binani ce ‘yar takarar APC a Adanawa, wato ranar 17 Ga Fabrairu.