Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso, ya ce idan ya zama shugaban ƙasa zai ƙyale kowa ya maida tsoffin kuɗin da ke hannun sa sannun a hankali a bankuna, ba cikin tashin hankali ba.
Ya ce an ƙirƙiro canjin kuɗi ne kawai don a ƙuntata wa talakawa.
Kwankwaso ya ce idan ya ci zaɓe zai ƙyale kowa ya ci gaba da amfani da tsoffin kuɗaɗen da ke hannun sa, daga baya a riƙa mayarwa bankuna a hankali.
Da ya ke tattaunawa a gidan talabijin na Channels, a ranar Juma’a, Kwankwaso ya ce talakan Najeriya ya bani ya lalace, domin duk wani tsari da ake ƙirƙirowa mai tsauri da tsanani, to kan talakawa ya ke ƙarewa.
“Tsarin sauya launin kuɗi shirme ne. Saboda waɗanda gwamnatin ke so ta kama a tsarin, ba za su taɓa kamuwa ba, domin su ne ke da bankuna.
“Idan na ci zaɓen shugaban ƙasa, zan ƙyale duk wani mai tsoffin kuɗi ya je banki hankali kwance ya canja kuɗaɗen sa a tsanaki, ba cikin hauragiya da tashin hankali ba.
Kwankwaso ya ce maganar gaskiya bai kamata a wahalar da talakawa ba, saboda talakawa su ne jigo kuma ƙashin bayan kamfen mu, inji Kwankwaso.
“Tsarin sauya launin kuɗi ba laifi ba ne, amma gutsiri-tsomar da ke tattare da tsarin musiba ce ga talakawa.” Cewar Kwankwaso.
Ya ƙara da cewa an shigo da tsarin a kuntaccen lokaci, da talakawa ke cikin ƙuncin rayuwa.
Haka kuma Kwankwaso ya tuna abin da ya kira “abin kunyar da ya faru a zaɓen gwamna a jihar Kano a 2019, wanda ya a sakamakon zaɓen Kano ya zubar da mutuncin INEC a 2019.
Sai dai kuma ya ce idan aka yi adalci a 2023, to INEC za ta farfaɗo da mutuncin ta.