Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya yi iƙirarin cewa wasu ‘yan ƙaƙuduba sun kewaye Shugaba Muhammadu Buhari, su na yi masa romon-bakan a san yadda aka yi zaɓe ya kasa gudana, sai a kafa gwamnatin riƙon ƙwarya kawai.
El-Rufai ya farrasa waɗannan ‘yan ƙaƙuduba da cewa wasu firɗa-firɗan ƙadangarun bariki ne kewaye da Buhari, waɗanda sagarabtun da su ke yi kewaye da shi ya yi daidai da irin ƙumbiya-ƙunbiyar masu neman yin amfani da farar hula su hamɓarar da mulkin farar hula, bayan zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa nan da makonni biyu.
“Sagwangwamai, alamomi da ‘yar manuniya sun fara bayyanar da labaran al’ajabi cewa akwai maƙarƙashiyar da wasu ‘yan ƙaƙuduba ke yi masu ganin sun dagula miƙa mulki bayan zaɓen 2023. Saboda kawai ba su so APC ta yi nasara. Wataƙila mugun nufin su idan zaɓe ya gagara, to sai a kafa gwamnatin riƙon ƙwarya.”
Haka El-Rufai ya shaida wa PREMIUM TIMES, cikin wata tattaunawar musamman da aka yi da shi, a ranar Lahadi.
Sai dai kuma ya ƙi bayyana sunayen waɗannan ‘yan ƙaƙuduba, waɗanda ya ce ‘yan-ta-kife ne kawai, ba wasu gingima-gingiman jiga-jigan siyasa ba ne a ƙasar nan.
El-Rufai ya ce su waɗannan ‘yan ƙaƙudubar ba su ma da basira da tunani irin na ‘yan ba-ni-na-iya ɗin da su ka amsa sunan su na ‘cabal’.
“Ba fa tsoron su na ke ba, kuma ba na tsoron bayyana sunayen su. Amma dai nawa tunanin gani na ke yi na ci baya idan na zo ina faɗin sunayen waɗanda ba su isa na ɓata lokaci kan su ba. Su da ba wata tsiya ba ce, babu mai iya cin zaɓe a cikin su. Ba su iya biya wa kan su wata buƙata, sai dai su jingina da Shugaba Buhari domin cimma wata buƙatar su kawai.”
El-Rufai ya nuna cewa babu wani dalilin da zai sa a ce wai Shugaba Buhari ba ya tare da takarar Tinubu.
“Da Buhari aka kafa APC, kuma tare da shi aka raine ta. Saboda haka ba zai taɓa yin abin da zai kawo wa APC ko ɗan takarar ta Bola Tinubu cikas ba.
“Yan ƙaƙudubar da ke kewaye da Buhari ba su ji daɗin ganin Tinubu ya lashe zaɓen fidda gwanin APC ba. Su na da na su ‘yan takarar a wancan lokacin, wato Gwamnan CBN Godwin Emefiele daga kudu, sai Ahmad Lawan daga Arewa. Amma sai ba su yi nasara ba.” Inji El-Rufai.
Ƙarin Bayani: A ɗan jira cikakkar tattaunawar nan da ‘yan kwanaki kaɗan, domin za a sha mamaki da al’ajabi.