Jami’ar Al-Qalam dake jihar Katsina ta bayyana cewa tana bin gwamnatin Kano bashin Naira miliyan 38 kudin makarantar dalibai.
Shugaban jami’ar farfesa Asiru Musa-Yauri ya sanar da haka ranar Alhamis da yake ganawa da manema labarai a garin Katsina.
Musa-Yauri ya ce a da bashin da Jami’ar ke bin gwamnati Kano ya zarce Naira miliyan 52.
Farfesan ya ce jami’ar na fama da matsalar rashin kuɗi saboda karancin kudin makarantar da ake biya a jami’ar.
“Zuwa yanzu muna sauraren gwamnatin Kano ta biya kudin karatun wasu dalibai ‘yan asalin jihar da ta dauki nauyin su a wannan Jami’a.
“Muna kira ga ƴan Najeriya su taimaka wa Jami’ar wajen yin kira da rokon gwamnatin jihar Kano ta biya Jami’ar wadannan kuɗaɗe da take bin ta.
Musa-Yauri ya yi kira ga gwamnatin da ta tausaya wa Jami’ar ta biya wadannan kudade ganin yadda jami’ar yanzu ke matsalar kuɗi.
Ya ce kudaden da gwamnatin za ta biya zai taimaka wajen inganta aiyukkan Jami’ar.
Kwamishinan ilimin jihar Kano Mariya Mahmoud-Bunkure ta ce ba ta da masaniya akan wani bashi da ake bin gwamnatin jihar.
Mariya ta ce kwanakin baya ta tattauna da Jami’ar kan yadda gwamnati za ta biya wadannan kudadeda bayan zaman da suka yi ta aika da rahoton abin da suka tattauna da Jami’ar wa gwamna Abdullahi Ganduje sannan har yanzu ba ta ji daga wajen sa ba tukunna.