Ƙaramin Ministan Ƙwadago, Festus Keyamo ya jinjina wa gwamnonin da su ka maka Shugaba Muhammadu Buhari kotu.
Festus Keyamo dai duk da haka bai ɗora laifin wahalar da jama’a ke sha a kan Buhari ba, amma ya ce ƙirƙiro canjin kuɗi ba zai iya hana APC cin zaɓen shugaban ƙasa ba.
“Idan da alheri Shugaban Ƙasa ya ƙirƙiro wannan tsari, to ai dama shi mutum ne mai yaƙi da rashawa, wanda duk Afrika ta shaida haka, ba Najeriya kaɗai ba.”
Gwamnonin APC a sahun gaban sukar canjin kuɗi daidai lokacin gabatowar zaɓe. Sai dai kuma a ɓangaren PDP ma Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto da Ademola Adeleke na Osun sun fito sun yi tir.
A tattaunawar da Minista Keyamo ya yi da Kamfani Dillancin Labarai (NAN) a ranar Asabar, ya ragargaji wasu ‘yan adawa masu sukar gwamnonin da ke la’antar sabon tsarin canjin kuɗi.
“Abin da ake ta magana a yanzu shi ne wai gwamnonin APC na ta fagamniyar neman kuɗaɗen da za su rabas ne domin su ci zaɓe ta hanyar sayen ƙuri’u, shi ya sa su ke ta haƙilon ganin lallai sai kotu ta soke tsarin.
“Abin da gwamnonin APC ke yi kishin ƙasa ne, ba wani abu ba.
Tuni dai gwamnoni irin na Kaduna, Zamfara da Kogi su ka maka Buhari kotu. Kuma gwamnonin na Kaduna, Kano da Jigawa sun bada umarnin dukkan masu tsoffin kuɗi su ci gaba da fito da su kuma tilas a riƙa karɓa, kafin a ji hukuncin da Kotun Ƙoli za ta zartas a ranar Laraba, 22 ga Fabrairu, 2023.
Discussion about this post