Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dage zabe a rumfunar zabe 141 a Yenegowa jihar Bayelsa.
Shugaban hukumar Mahamood Yakubu wanda ya sanar da haka a Abuja ya ce hakan ya auku ne a dalilin tashin hankali da aka samu a unguwanni 4,6,8 da 14 inda a yanzu haka jami’an tsaro sun ce sun shawo kan matsalar
“Mun yanke hukuncin cewa za a ci gaba da zabe a wadannan unguwanni gobe ranar Lahadi inda rumfuna 40 daga cikin rumfunan zabe 141 sun rasa kayan akin zabe saboda hatsaniyar.
Dage zaben da hukumar ta yi ya shafi zaben Shugaban kasa da na ‘yan majalisar wakilai a wadannan unguwanni wanda za a yi gobe Lahadi.
Bayan haka Yakubu ya ce hukumar zaben ta rasa naurorin BVAS a dalilin harin da ‘yan jagaliya suka kai rumfunar zabe a fadin kasar nan.