Jigon jam’iyyar PDP Dino Melaye, ya yi kira da kakkausar murya cewa lallai a dakatar da bayyana zaɓen da hukumar zaɓe ke yi a Abuja, cewa an yi wa jam’iyyar sa ta PDP ƙwange da cuwacuwa.
Dino ya bayyana cewa dokar hukumar zaɓe ta ce lallai duk sakamakon da za a bayyana a tabbatar sakamakon nan ya biyo ta rumbun tattara zaɓe dake yanar gizo wanda ke a hukumar INEC ɗin.
Ya ce a wurare da dama an yi aringizon ƙuri’u rututu sannan ba ayi amfani da na’urar tantance masu jefa ƙuri’a ba kafin a bayyana sakamakon zaɓe.
Dino ya ce za su mika koken su ga shugaban hukumar zaɓe idan aka dawo daga hutun a ɗan natsa.